Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ‘ta kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye da 1000 a shekara ɗaya’

Dakarun sojin sun kuma kwato harsasai fiye da 24,000, tare da lalata bama-bamai da aka ƙera su a gida, wato IED, 295. Ya ce an kama mutane 758 da ake zargi da taimakawa ‘yan ta’adda wajen safarar makamai da sauran kayan aiki.

Newstimehub

Newstimehub

16 Sep, 2026

9a0f9b60 1ff8 4407 b097 d5e09a4347bd 1789534281856

Rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin Nijeriya ta ce dakarunta da ke aiki a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar sun kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP aƙalla 1,106 tare da ƙwato makamai fiye da 475 a cikin shekara guda.

An bayyana hakan ne yayin bikin miƙa ragamar jagorancin Rundunar da Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya yi ga Manjo Janar Ibikunle Ajose a Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar Talata.

Kazalika Manjo Janar Abubakar ya ce sojojin sun ƙwato harsasai fiye da 24,000, tare da lalata bama-bamai da aka ƙera su a gida, wato IED, 295.

Ya ce an kama mutane 758 da ake zargi da taimaka wa ‘yanta’adda wajen safarar makamai da sauran kayan aiki.

Ya ƙara da cewa mayakan JAS da ISWAP 969 da iyalansu sun miƙa wuya cikin shekara guda, yayin da aka ceto fararen-hula 638 daga sansanonin ‘yanta’adda.

Kwamandan mai barin gado ya ce ayyukan sojojin sun taimaka wajen mayar da iyalai fiye 7,000 da suka rasa matsugunansu zuwa garuruwansu a jihar Borno.

Ya kuma ce an sake buɗe kasuwanni da hanyoyin kasuwanci, tare da dawo da shirin horas da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) zuwa Maiduguri bayan shafe fiye da shekaru 13.

An kuma dawo da gudanar da jarrabawar WAEC da NECO a wasu yankunan da suka haɗa da Banki da Gwoza.

Haka kuma, rundunar ta bayyana ƙwato Naira miliyan 300 da ake zargi suna da alaƙa da masu ɗaukar nauyin ‘yanta’adda, tare da taimakawa wajen dawo da wasu ‘yan Nijeriya fiye da 3,000 daga ƙasar Kamaru.

A nasa ɓangaren, sabon kwamandan rundunar, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya yi alƙawarin ƙarfafa nasarorin da aka samu tare da ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya tare da ganin harkokin tattalin arziki sun bunƙasa a Arewa Maso Gabas.

Ajose, wanda ya taɓa riƙe muƙamai a jihar Borno, ya ce zai ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar da ƙungiyoyin agaji da rundunar haɗin gwiwa ta farar-hula da kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da ta’addanci a yankin.