Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana tunanin tura karin jiragen yaƙi na ruwa da jirgin sama mai ɗaukar jiragen yaƙi zuwa Gabas Ta Tsakiya, a daidai lokacin da ake ci gaba da tantance matakan tsaro dangane da Iran.
A wata hira da Axios, Trump ya ce ayarin jiragen yaƙi na kan hanyarsa zuwa yankin, kuma wani karin ayari na iya biyo baya. Wannan mataki zai haɗu da jirgin yaƙi na USS Abraham Lincoln da dakarunsa, a wani yanayi mai kama da yadda aka ƙara karfin soji a lokutan rikici a baya.
Matakin na zuwa ne yayin da ake sake farfado da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran, bayan ganawar jami’an ɓangarorin biyu a Oman. Trump ya ce ko dai a cimma yarjejeniya ko kuma a ɗauki mataki mai tsauri, yana mai nuna fata kan ci gaban tattaunawa.
Tehran ta jaddada cewa tattaunawar za ta ta’allaka ne kan shirin nukiliyarta kawai, tare da nacewa kan ’yancinta na sarrafa yuraniyom.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














