Masu shiga tsakani a yankin suna kokarin sassauta zaman tankiyar da ke ruruwa tsakanin Amurka da Iran, yayin da suke kiran da a ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliya, kamar yadda shafin labarai na Axios ya ruwaito ranar Alhamis.
Majiyoyi da dama, guda biyu daga kasashen da ke shiga tsakani sannan guda daya kuma jami’in Amurka, sun shaida wa kafar yada labaran cewa gwamnatocin yankin suna ta kokarin kwantar da tarzoma tsakanin kasashen biyu.
Wata majiya ta shiyya daga daya daga cikin kasashen da ke shiga tsakani ta bayyana cewa, masu shiga tsakanin sun yi amannar cewa hare-haren da Iran ta kai a baya-bayan nan a Mashigin Tekun Hormuz, wasu bangarori ne na cikin gwamnatin Iran da ke adawa da yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran suka kai su, kuma suna neman lalata yarjejeniyar ne.
Majiyoyin sun ce jami’ai daga kasashen Qatar, Pakistan, Masar, da Saudiyya sun gudanar da tattaunawa ta wayar tarho da dama da jami’an Amurka da na Iran a ranar Laraba, a matsayin kokarin kwantar da rikicin.
“Akwai gagarumar fafutuka ta diflomasiyya da farko domin cimma daidaito da bangarorin biyu kan kwantar da tarzoma, sannan daga baya a tsaida lokaci don gudanar da wani zagaye na tattaunawa tsakanin kwararrun masana na bangarorin biyu,” in ji wata majiya ta shiyya da ke da hannu a shiga tsakanin.
Iran da Amurka sun yi musayar hare-hare a cikin kwanaki biyu da suka gabata, a daidai lokacin da takaddama ta kazance biyo bayan hare-haren da Iran ta kai kan wasu jiragen ruwa na kasuwanci guda uku a Mashigin Tekun Hormuz.
Gwamnatin Iran ta kaddamar da jerin hare-hare a ranar Alhamis kan dakarun sojin Amurka da ke kasashen Bahrain, Kuwait, Qatar, da Jordan, a matsayin maida martani ga hare-haren dare da Amurka ta kai musu har na tsawon kwanaki biyu a jere.
















