Majalisar Dokokin Nijeriya ta aika da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar da zai ba da damar kafa rundunonin ’yansanda na jihohi ga majalisun dokokin jihohi 36 domin amincewa da shi.
Matakin na zuwa ne a wani lokaci da Shugaba Bola Tinubu ke fuskantar ƙarin matsin lamba kan yadda ake tunkarar matsalar rashin tsaro a ƙasar, gabanin zaɓukan watan Janairu.
Magatakardar Majalisar Dokokin Najeriya, Kamoru Ogunlana, ya ce Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na Shida na 2026, wanda ya ƙunshi tanadin kafa ’yansandan jihohi, ya samu amincewar ’yan majalisar tarayya kuma yanzu an aika shi ga majalisun jihohi domin su yi nazari da kuma yanke matsaya.
Ogunlana ya ce an buƙaci majalisun jihohin su mayar da matsayarsu cikin kwanaki 30, sai dai ya ƙara da cewa wa’adin na gudanarwa ne kawai, kuma kundin tsarin mulki bai ɗaure majalisun da wannan wa’adi ba.
Domin kudirin ya zama doka, dole ne a samu amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohin ƙasar, wato jihohi 24 daga cikin 36.
Masu goyon bayan kafa ’yan sandan jihohi na cewa matakin zai taimaka wajen inganta martanin hukumomin tsaro ga barazanar da ta shafi al’ummomin yankuna daban-daban, ta hanyar karkatar da wasu ikon kula da tsaro daga gwamnatin tarayya zuwa jihohi.
Sai dai kafa rundunonin ’yan sandan jihohi na daga cikin manyan batutuwan da aka daɗe ana muhawara a kansu a Najeriya, musamman kan yadda za a tabbatar da cewa rundunonin ba za su zama kayan siyasa ko kuma su yi aiki ba tare da isasshen sa ido ba.
Baya ga kudirin kafa ’yansandan jihohi, wasu kudirorin gyaran kundin tsarin mulki da ke jiran amincewa ta ƙarshe sun haɗa da ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, takarar ’yan takara masu zaman kansu, ware kujerun majalisa ga mata, da ba da damar samun ɗan ƙasa ta hanyar zuba jari.
Idan adadin jihohin da kundin tsarin mulki ya tanada suka amince da kudirin, hakan zai zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi wa tsarin tsaro da mulki a Najeriya tun bayan komawar ƙasar tsarin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

















