Nijeriya

Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗau mataki bayan litar mai ta kai N1,500

Ƙungiyar NLC, a wata sanarwar da shugabanta, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu ranar Laraba ta ce a halin yanzu ana sayar da litar man fetur ne kan kuɗi naira 1,430 a muhimman birane.

Newstimehub

Newstimehub

17 Sep, 2026

53fd8f63 01a8 4c05 8e11 fca37839ca89 1786349015806

Farashin man fetur ya ci gaba da tashi a faɗin Nijeriya inda ake sayar da litar man kan kuɗi N1,500 a jihohin Kano da Yobe da Sokoto da Borno da Taraba da kuma Zamfara, yayin da farashin ya kuma tashi sosai a cikin sauran sassan ƙasar.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Ƙungiyar ƙwadagon ƙasar take kira ga wamnatin ƙasar ta ɗauki matakan gaggawa na rage raɗaɗin tashin farashin man fetur, ciki har da biyan albashin da ya kamata ga ma’aikata da kuma sayar da ɗanyen ga matatun man cikin gida da kudin naira.

Ƙungiyar NLC, a wata sanarwar da shugabanta, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu ranar Laraba ta ce a halin yanzu ana sayar da litar man fetur ne kan kuɗi naira 1,430 a muhimman birane, inda rahotanni suka nuna cewa farashin ya fi hakan a wasu wuraren da suka fi nisa a ƙasar.

Ƙungiyar ƙwadagaon ta yi gargaɗin cewa tashin farashin mai ɗin zai iya ƙara tsananta masin tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, tana mai cewa tashin farashin sufuri na ƙara farashin kayayyakin abinci da kuɗin haya da kuɗin makaranta da sauran ababen buƙata ta yau da kullum.

Bugu da ƙari, ƙungiyar masu sayar da man fetur ita ma ta bi NLC wajen kira ga Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta shiga kasuwar man fetur ɗin, tana mai gargaɗin cewa farashin man zai iya kaiwa naira 2,000 kan kowace litar man fetur idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da tashi a kasuwar duniya, yayin da masu ruwa da tsaki ke kira ga gwamnati ta rage tasirin matatar man Dangote da ke ƙaruwa kan kasuwar.

Buƙatun NLC

A wata sanarwa mai taken “Kare yanayin a yanzu,” ƙungiyar NLC ta ce ƙarin farashin mai na baya bayan nan na zuwa ne a wani lokaci da matsin da gwamnati ta yi wa masu sayar da man na rage farashin mai sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar Duniya ya fara nuna sakamako.

NLC ta ce duk da cewa an alaƙanta tashin farashin mai na baya bayan nan da rikicin yankin Gulf, amma matsayin Nijeriya na ƙasa mai samar da mai na nufin ya kamata ta iya samar da wani nau’i na kariya daga girgizar kasuwar duniya.

Ta ce, “A matsayin ƙasa, da kuma wasu mutane da aka yi wa baiwar makamashi, mun dace mu sami wani mataki na kariya ko kuma shinge daga guguwar da ke kaɗowa daga yankin Gulf da ma guguwa daga sauran wurare.”

NLC ta yi kira ga gwamnatin Tarayyar ta gabatar da mataki na kariya nan take domin kare gidaje da masana’antu daga tasirin tashin farashin man fetur.

Ƙungiyar ta yi kira da a ba da albashin da ya dace ga ma’aikata da kuma sayar da isasshen ɗanyen mai ta naira ga matatun mai na cikin gida da kuma faɗaɗa ƙarfin ajiyar man ƙasar domin ƙarfafa tsaron makamashi da kuma shiryawa domin ko ta kwana.

Ƙungiyar ƙwadagon ta ce matakan ba kawai za su rage wa ‘yan Nijeriya nauyi ba ne, amma za su samar da ayyukanyi da samar da kimar tattalin arziki da kuma taimaka wajen magance matsalolin tsrao da ke tasowa.

Ta kuma ce kawo ɗaukin gwamnatin ciki har da tallafi abu ne da bai kamata a kore ba a lokacin buƙatar taimakon gaggawa.

“Babu wata matsala idan gwamnati ta ba da tallafi ga buƙatun ‘yan ƙasa, musamman a wani lokaci na buƙatar taimakon gaggawa irin wannan,” kamar yadda Ajaero ya bayyana, yana mai ƙarawa da cewa ƙasashe masu samar da mai suna ƙaddamar da shirye-shirye na tallafi domin kare ‘yan ƙasashensu daga tasirin matsalar makamashi ta duniya ta yanzu.

NLC ta ƙara da cewa gwamnatin tarayyar ƙasar amfana daga tashin farashin ɗanyen mai, tana mai iƙirarin cewa farashin ɗanyen mai a yanzu ya ɗara farashin da aka yi kasasfin kuɗi ƙasar a kai da kimanin $35 zuwa $40 kan ko wace gangar ɗanyen mai.

Saboda haka, ya kamata mutanen ƙasar su ma su amfana da abin da wamnatin ta samu, in ji ƙungiyar ƙwadagon.