Nijeriya

Nijeriya ta tura sojoji 86 domin aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau

Tawagar wadda ta ƙunshi sojoji 86 ta tashi daga filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Asabar.

Newstimehub

Newstimehub

2 Aug, 2026

82064dfb 970f 45d7 bf42 10fd944e7e0f 1785679217610

Nijeriya ta tura wata tawaga ta sojojin ƙasar zuwa Guinea-Bissau domin aikin wanzar da zaman lafiya a ƙasar a ƙarƙashin ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS.

Tawagar wadda ta ƙunshi sojoji 86 ta tashi daga filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Asabar.

Jirgin rundunar sojojin saman Nijeriya, wanda ke ɗauke da dakarun ƙasar, ya isa Guinea-Bissau, inda za su soma aiki nan-take.

Kafin tashin dakarun na Nijeriya, babban kwamandan dakarun wanzar da zaman lafiya da ke Abuja, Manjo Janar M.L.D. Saraso, wanda ya samu wakilcin Birgediya Janar M.M. Idris, ya umarci sojojin su nuna halaye na gari da ƙwarewa yayin gudanar da ayyukansu.

Kazalika ya umarce su da su yi biyayya ga dokoki da al’adun ƙasarm sannan su guji yin lalata ko shaye-shaye ko kuma bayyana halayen banza a shafukan sada zumunta.

Rundunar sojin Nijeriya ta ce wannan aiki ya nuna yadda ƙasashen yankin suke girmama ƙasar a ƙokarinta na wanzar da zaman lafiya a ƙasashen nahiyar.