Afirka

Jamhuriyyar Kongo da ‘yan tawayen M23 sun cim ma yarjejeniya domin dakatar da rikici a gabashin DRC

An cim ma yarjejeniyar ne bayan ɓangarorin biyu sun shafe watanni uku suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar.

Newstimehub

Newstimehub

19 Jul, 2025

1752917849038 a4ov3d bf5b8be7cde684fb3aaed05d3451654a42ea29a71e3af2993561a772adb58d67

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da ƙungiyar ‘yan tawayen M23 da ake zargin tana samun goyon bayan Rwanda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Asabar, domin kawo ƙarshen rikicin da ya addabi gabashin ƙasar mai arzikin ma’adanai amma cike da rikice-rikice.

An cim ma yarjejeniyar ne bayan ɓangarorin biyu sun shafe watanni uku suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar. Wannan na zuwa ne bayan wata yarjejeniya ta daban da aka cim ma tsakanin Congo da Rwanda a birnin Washington a watan da ya gabata.

Kungiyar M23, wadda ta mamaye manyan yankuna a gabashin DRC cikin wata guda a watan Janairu da Fabrairu, inda ta dage kan cewa tana son ƙulla yarjejeniya ta musamman da gwamnatin Kinshasa, saboda yarjejeniyar Washington ta bar wasu “muhimman matsaloli” a gefe.

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yaba da wannan ci gaba, tana mai cewa:

“Wannan muhimmin ci gaba ne da ke nuna sahihancin ƙoƙarin kawo zaman lafiya da dawwamammen tsaro a gabashin DRC da kuma yankin Great Lakes

A cewar yarjejeniyar, bangarorin sun kuma amince da fara tattaunawa don ƙulla cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya, tare da samar da taswirar dawo da ikon gwamnati a yankunan gabashin DRC da ke ƙarƙashin ikon ‘yan tawaye.