Gabas Ta Tsakiya

Wata ƙungiyar bayar da agaji ta Turkiyya ta ƙaddamar aikin kwashe ɓaraguzai a arewacin Gaza

Wannan shirin, wanda aka fara a ranar Asabar, ya mayar da hankali kan tsaftace muhalli, cire tarkace, da kuma buɗe hanyoyin da aka toshe, inda aka fara aikin a arewacin Gaza, ɗaya daga cikin wuraren da suka fi shan wahala, kamar yadda IHH ta bayyana.

Newstimehub

Newstimehub

19 Oct, 2025

5ddd026fb647b5d6c40d38fdec3ee14c8c5d1c40d2b05a2c79924631ce1c4f8a

Kungiyar Agaji ta Turkish Humanitarian Relief Foundation (IHH) ta sanar da ƙaddamar da wani sabon shiri a Gaza wanda aka tsara domin magance mummunar ɓarnar da hare-haren Isra’ila suka haifar a wannan yankin da aka yi wa ƙawanya na Falasdinawa.

Wannan shirin, wanda aka fara a ranar Asabar, ya mayar da hankali kan tsaftace muhalli, cire tarkace, da kuma buɗe hanyoyin da aka toshe, inda aka fara aikin a arewacin Gaza, ɗaya daga cikin wuraren da suka fi shan wahala, kamar yadda IHH ta bayyana.

An tura manyan injina da ƙungiyoyin ƙwararru don cire tarkace daga unguwannin zama, domin tabbatar da cewa tituna da wuraren jama’a sun sake zama masu amfani ga mutane.

665093241b44ac9190fb3997d9f78c66f26d7fc97aa04f3d31823be6e1319960

Kungiyar ta jaddada cewa aikin ba kawai gyaran gine-gine bane, har ma da dawo da yanayin rayuwa da kuma tabbatar da tsaro ga mazauna Gaza.

1485ab88375cd14856b726ff7f1c9b0bd71bedcdfcb96a0c0760467cb171ac75

IHH ta bayyana cewa bude hanyoyin shiga da fita yana da matuƙar muhimmanci wajen sauƙaƙa kai agaji, musamman wajen isar da abinci, kayan magani, da sauran abubuwan buƙatu da ake buƙata cikin gaggawa ga al’ummomin da aka daɗe da katse kai musu kayayyaki.

Ƙungiyar ta kasance tana aiki a Gaza tsawon shekaru, tana bayar da tallafi a fannoni kamar rabon abinci, samar da mafaka, ayyukan tsafta, kula da lafiyar ƙwaƙwalwa, da shirye-shiryen kiwon lafiya.

Tare da wannan sabon aikin na cire tarkace da buɗe hanyoyi, ƙungiyar ta ce tana fatan hanzarta gyaran muhalli a biranen Gaza da kuma taimakawa wajen inganta yanayin rayuwar dubban Falasɗinawa.