Rundunar Sojin Nijeriya ta fito fili ta karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa wani matashi daga Jihar Gombe, Ibrahim Nazifi, ya mutu yayin atisayen horaswa a Depot na Zaria. Rundunar ta bayyana labarin a matsayin ƙarya mara tushe da kuma ruɗani ga jama’a.
A cikin wata sanarwa da sansanin horaswar ya fitar, an ce Nazifi, mai lambar rajista 90RRI-GO-9017726, ya tsallake tantancewar ɗaukar sojoji a watan Disamba 2025, amma bai taɓa halartar horo a Depot na Zaria ba, balle a ce ya rasu a can. Rundunar ta jaddada cewa babu wani rahoto na rauni ko mutuwa da ya shafi shi a sansanin.
Sojojin sun buƙaci Gwamnatin Jihar Gombe da sauran hukumomi da su binciki inda labarin ya samo asali, tare da tabbatar wa al’umma cewa atisayen soja na gudana ne ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro da kulawar lafiya.














