Ƙasar Saudiyya ta yi kira ga dakarun Rapid Support Forces (RSF) da su gaggauta dakatar da abin da ta bayyana a matsayin mummunan take hakkin fararen hula a yankin Darfur na Sudan. Wannan kiran ya zo ne a Geneva bayan jawabin Babban Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya kan Hakkokin Bil Adama, Volker Türk, wanda ya ɗora alhakin “mugayen laifuka” da aka aikata a Al Fasher kan RSF da abokanta. Riyadh ta yi tir da hare-haren da aka kai kan asibitoci, motocin agaji da wuraren fararen hula, tana mai cewa an samu asarar rayuka ciki har da mata da yara.
Saudiyya ta jaddada wajabcin bin dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, musamman wajen tabbatar da isar da agaji cikin aminci. Rikicin ya kara tsananta bayan RSF ta ƙwace ikon Al Fasher a Oktoban 2025, yayin da faɗa ke yaɗuwa zuwa jihohin Kordofan. Yaƙin da ya ɓarke tun 2023 tsakanin RSF da sojin Sudan ya riga ya haddasa mutuwar dubban mutane tare da tilasta kusan miliyan 13 barin gidajensu, lamarin da ya jefa ƙasar cikin mummunar matsalar jin kai.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














