Wani sabon binciken jin ra’ayin jama’a na NBC News ya nuna cewa yawancin masu kada kuri’a a Amurka ba su amince da yadda Shugaba Donald Trump ke tafiyar da rikicin da ke tsakaninsa da Iran ba. Binciken ya nuna cewa kashi 54 cikin 100 ba su gamsu da manufarsa ba, yayin da kashi 41 cikin 100 suka nuna goyon baya.
Haka kuma, fiye da rabin masu kada kuri’a sun ce bai kamata Amurka ta fara kai hare-haren soji kan Iran ba. A cewar sakamakon binciken, kashi 52 cikin 100 sun nuna adawa da irin wannan mataki, yayin da kashi 41 cikin 100 suka ce suna goyon bayansa.
Ra’ayoyin jama’a sun bambanta sosai bisa ga bangaren jam’iyya. Yawancin ‘yan Republican sun goyi bayan matakin soji, musamman masu goyon bayan akidar MAGA, inda kusan kashi 90 cikin 100 suka ce harin ya dace. Sai dai wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar ma ba su gamsu da shiga yakin ba.
Binciken ya kuma nuna cewa a tarihi Amurkawa kan nuna goyon baya ga matakan soja a farkon rikici, kamar yadda aka gani a yaƙin Afghanistan da na Iraki, amma wannan goyon baya kan ragu bayan lokaci yayin da sakamakon yaƙin ke bayyana.














