Gabas Ta Tsakiya

Isra’ila ta yi asarar $57bn a tattalin arzikinta cikin shekara biyu kan kisan kiyashin Gaza

Alƙaluma daga babban bankin Isra’ila sun nuna muhimmin asarar tattalin arziki da aka alaƙanta da kisan kiyashin Gaza da rikicin yankin.

Newstimehub

Newstimehub

24 Mar, 2026

1774307863535 w931fr 33d0e1d90b3ac9ff456678d68dfa02281febc8f5e534b97f6c8fcad4d39af250

Tattalin arzikin Isra’ila ya tafka asarar da ta zarce ta dala biliyan 57 cikin shekara biyu na kisan ƙare-dangi a Gaza, in ji wani rahoton da kafar Bloomberg ta wallafa.

Alƙaluman da aka wallafa a shekarar 2025 a cikin rahoton shekara-shekara na babban bankin Isra’ila sun nuna asarar sehekl biliyan 177, wanda ya yi daidai da dala biliyan 57 ko kuma kashi 8.6 cikin 100 na ƙimar tattalin arzikin ƙasar a ma’aunin GDP, tsakanin shekarar 2023 zuwa shekarar 2025.

An alaƙanta yawancin asarar ne da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma harin da Isra’ila ta kai Lebanon.

Rahoton bai haɗa da tasirin tattalin arziki na yaƙin da ake yi a Iran ba, wanda ya shiga makona na huɗu, kuma Isra’ila take kai hare-haren sama ko da yake tana fuskantar hare-haren ramuwar gayya.

A farkon wannan watan, majalisar zartarwar yaƙi ta Isra’ila ta amince a sabunta kasafin kuɗi na ƙasa na shekarar 2026, inda ta ƙara dala biliyan 13 domin a kasafin kuɗin yaƙinta.

Rahoton ya kuma nuna sauyi a yanayin cinikayya, inda fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen Tarayyar Turai takwas wanda ake ganin sun fi muhimmanci ga Isra’ila ya faɗi da dala biliyan ɗaya a shekarar 2024 da kuma dala biliyan $1.5 a shekarar 2025, yayin da cinikayya da sauran ƙasashe ya ƙaru.

“Wannan yanayin zai iya nuna cewa matsayar siyasa na tasiri kan adadin abin da ake fitarwa zuwa waɗannan ƙasashen,” in ji babban bankin na Isra’ila.

Ya ƙara da cewa yaƙin kwanaki 12 da Iran a watan Yunin da ya gabata kaɗai ya rage tattalin arzikin ƙasar da kashi 0.3 cikin 100 na kimar tattalin azikin ƙasar a ma’aunin GDP.

Isra’ila ta ƙaddamar da kisan ƙare danginta ne kan Gaza a watan Oktoban shekarar 2023, inda ta kashe fiye da Falasɗinawa 72,000 , inda ta jikkata kimanin 172,000 tare da lalata kimanin kashi 90 cikin 100 na ababen more rayuwa na fararen hulan birnin..