Gabas Ta Tsakiya

‘Ba za a iya ƙwace Hormuz ta saƙon X ko jirgin dakon jiragen yaƙi ko jawabin zaɓe ba’ — Iran

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi ya yi kira ga Amurka ta amsa shan kaye bayan Shugaba Trump ya sha alwashin karɓe iko da Mashigar Hormuz da kuma mayar da ita wani yanki na ƙasar Amurka.

Newstimehub

Newstimehub

15 Aug, 2026

351843f7 31b8 4954 b046 a29b7b0d3c9c 1781478991267

Da yake watsi da kalaman Shugabn Amurka Donald Trump cewa shi zai ayyana Mashigar Hormuz a matsayin wani yanki na ƙasar Amurka, wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya jaddada cewa mashigar ta Iran ce kawai kuma ya yi kira ga Amurka ta amsa shan kaye a yaƙin da take yi da Iran.

“Ba za a iya ƙwace Mashigar Hormuz ta saƙon X ko jirgin dakon jiragen yaƙi ko kuma umarni ko kuma wani jawabin zaɓe ba,” kamar yadda Mataimakin Ministan Harkokin Waje Kazem Gharibabadi ya rubuta a kan shafin kamfanin sada zumunta na Amurka X ranar Jumma’a, yana mai ƙarawa da cewa, “Iran ba ta tsoron barazana kuma ba za a iya saka mata tsoro a zuciya ba ta hanyar nuna ƙarfi.”

Gharibabadi ya rubuta cewa: “Mashigar Hormuz ta kasance ƙasar Ira, ta Iran ce, kuma za ta ci gabada kasancewa ƙasar ta Iran. Za a iya buɗe ko rufe wannan mashigar ne kawai bisa umarnin Iran har sai kun yarda da gaskiyar shan kayenku kuma kuka yi watsi da tunanin mafarkinku, Iran za ta ci gaba da ƙaƙaba ƙawanya (kan Hormuz).”

A wata sanarwar da ya fitar da yammacin ranar Jumma’a, Trump ya ce rundunar sojin ruwan Amurka tana ƙaƙaba cikakken ƙawanya kan Mashigar Hormuz kuma ya tabbatar da cewa: “Bayan mun yi cikakkiyar nasara a kan Iran, za ni ayyana Mashigar Hormuz wani yanki na ƙasar Amurka ba da jimawa ba.”

Trump ya kuma yi kira ga Amurkawa su karɓi ɗan ƙarin farashin kuɗin mai yayin da yaƙi kan Iran ɗin ke ci gaba.

Jami’an Iran suna ci gaba da nanata cewa ba za a sake buɗe mashigar ba idan har Amurka ta ci gaba da shiga lammura a yankin kuma ta ci gaba da ƙaƙaba ƙawanya da kuma gazawa wajen cika sharruɗan tsarin yarjejeniyar watan Yuni tsakanin Tehran da Washington.

Trump, a kan shafin sada zumuntansa na Truth Social, ya ce Amurka tana da “cikakken iko ” a kan Mashigar Hormuz kuma ya yi imanin cewa za ta iya ci gaba da rike ikon.

Ibrahim Zolfaqari, mai magana da yawun hedikwatar tsaro ta Khatam al-Anbiya, babban hedikwatar tsaron sojin Amurka da ke jagorantar yaƙin, ya bayyana ranar Jumma’a cewa : “Babu wani jirgi da za a bari ya wuce ta Mashigar Hormuz ba tare da izinin Iran da kuma sa-idonta ba.”

Kaikomo ta Hormuz ya ragu

A halin yanzu, jirage biyu ne kawai suka wuce ta Mashigar Hormuz ranar Jumma’a, in ji bayanai da aka samu daga kamfanin Kpler mai bibiyar tafiyar jirage: wani jirgi na hatsi da yake shiga ruwan Iran da kuma wani jirgi fanko da ke tafiya ta ɗaya ɓangaren.

Wani jirgi fanko na ɗaukar kayayyakin fetur da ke tafiya yankin Gulf ta mashigar, kamar yadda bayanai suka nuna. Babu wata jigilar ɗanyen mai da za a iya gani.

Wasu jiragen ruwa za su iya wucewa ta mashigar ba tare da an gane su ba idan sun kashe nau’urar ba da bayanansu, amma adadinsu bai kai ko kusa da adadin jiragen ruwa 130 da suke bin mashigar a kullum kafin yaƙin ba.

Kamfanin mai na ƙasa na Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya ce an kai hari kan biyu daga cikin jiragen ruwanta da ke wucewa ta mashigar ranar Alhamis da yamma, sannan kamfanin dillancin labaran daular WAM ya ba da rahoton cewa an kai hari kan wani jirgin na daban kuma ranar Jumma’a.

Iran ta bayyana abin da ta ƙaƙaba kan kaikomo ta mashigar a matsayin rufewa, yayin da Amurka take amfani da kalmar wajen bayyana barazanarta kan jiragen Iran da ke barin tashoshin jiragen ruwanta.

Yayin da yarjejeniyar na wucen gadi na watan Yuni ke gab da wargajewa, babu wata alama mai nuna cewa Amurka ko Iran na shirin sake fara tattaunawar zaman lafiya.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kawo yanzu ba a yanke wata shawara ba game da sake fara tataunawa da Amurka, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran ya ruwaito ranar Asabar.

Masu shiga tsakani Qatar da Pakistan sun kasance suna tuntuɓar Iran kuma suna musayar saƙonnin, amma wannan bai zamto tattaunawa ba, in ji Aragchi.