Ma’aikatan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun kama wata tsohuwa mai shekara 101 saboda zarginta da sayar da tabar wiwi a karamar hukumar Ilisan ta Jihar Ogun.
An kama ta ne a ranar 15 ga Agustan 2026 da wani nau’in wiwi mai nauyin giram 90. hukumar ta ce dattijuwar tana sayar da tabar wiwi ɗin ne kaɗan-kaɗan.
A cewar NDLEA, matar mai shekaru da fiye 100 ta shaida wa masu bincike cewa ta shiga harkar sayar da miyagun ƙwayoyi ne bayan gobara ta lalata shagonta na sayar da kayan abinci.
Ta bayyana cewa ‘yarta, wacce ke zaune a jihar Legas ce take samar mata da wiwi duk bayan kwana huɗu don ta sayar wa abokan cinikayyarta a yankin da take.
Bayan kama ta da aka yi, Shugaban Hukumar NDLEA ta ƙasa, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya ba da umarnin a ba da belinta kuma a ba ta shawara tare da gargaɗinta saboda tsufanta.
An kama ‘yarta daga baya bisa zarginta da ta’ammali da kuma kasuwancin miyagun ƙwayoyi.

















