Wata ƙungiya ta’addanci ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda mazauna wani yanki a jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Nijeriya suka ce an sace mata da yara da kuma tsofaffi har 600 a harin da aka kai wani masallaci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Bidiyon, wanda aka wallafa a ranar Lahadi a shafin Facebook da WhatsAp, ya nuna yadda wasu mutane masu yawa ke zaune a wani daji da ke kewaye da miyagun mutane ɗauke da makamai, in ji rahoton Reuters
Kana, an ga yara da dama suna kuka a baya.
Ko da yake Reuters bai iya tabbatar da sahihancin bidiyon ba, saboda ‘yansanda da hukumomin jihar ba su amsa buƙatar samun ƙarin bayani ba.
Matsalar satar mutane don neman kuɗin fansa ta zama ruwan dare a sassan arewa maso yamma da arewa maso tsakiyar Nijeriya, inda ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke yawan kai hare-hare a ƙauyuka da makarantu da kuma manyan hanyoyi.
Haka kuma bidiyon ya bayyana ne kwana biyu bayan wasu’yanbindiga sun kai hari yayin da mutane ke gudanar da sallar Jumma’a a masallacin da ke ƙauyen Dekara, kana suka yi awon-gaba da mutane da dama, lamarin da mazauna yankin suka ce ana yawan samu.
‘Yansanda sun tabbatar da harin da aka kai wa masu ibada a yankin amma sun ce ba za su iya tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.
A cikin bidiyon, an ga wani ɗanbindiga yana magana da harshen Hausa inda yake kira ga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su tare da shaida musu su duba ‘yan’uwansu daga cikin mutanen da ke cikin bidiyon.
“Waɗannan duk mutanenku ne. Muna nuna muku wannan bidiyon ne domin ku iya gano ‘yan’uwanku da iyayenku maza da mata da ‘ya’yanku da kuma danginku,” in ji ɗanbindigar.
Wani mazaunin yankin mai suna Jamilu Ibrahim ya roƙi hukumomin tarayya da na jiha da su tabbatar da an saki waɗanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.

















