Nijeriya

‘Yansandan Nijeriya sun gano ƙoƙon kawuna 28 a wani daji a Jihar Abia

Rundunar ‘yansandan ta ce waɗanda suke zama a maɓoyar sun tsere ne yayin da jami’an tsaro suka isa dajin.

Newstimehub

Newstimehub

29 Sep, 2026

28eae140 d6ad 4680 a252 1d3d9ae28af2 1789079936977

An gano ƙoƙon kawunan mutane 28 da sauran ƙasusuwa yayin samamen da ‘yansandan Nijeriya suka kai a wata maɓoyar masu aikata laifi a dazukan Umuaku-Isuochi da Nneato a ƙaramar hukumar Umunneochi ta jihar Abia a kudu maso gabashin ƙasar.

Rundunar ‘yansandan jihar ta ce an samu gawargawakin mutanen ne yayin samamen da aka kai bisa samun bayanan sirri ranar Lahadi a wani ɓangare na ayyukan da take yi na wargaza dukkan dabar masu aikata laifuka a faɗin jihar.

Rundunar ta ce, jami’ai na musamman na ɓangaren yaƙi da laifuka da garkuwa da mutane da na ko-ta-kwana da kuma na hedkwatar rundunar ne suka yi aikin.

Rundunar ‘yansandan ta ce waɗanda suke zama a dabar sun tsere ne yayin da jami’an suka isa dajin.

“Da jami’ai na musamman ɗin suka isa dabar, waɗanda ake zargin sun tsere. Daga bisani aka lalata dabar,” in ji mai magana da yawun rundunar, Maureen Chinaka.

Yayin bincike a dabar da aka bari babu kowa ne jami’an sun gano gawarwakin mutanen da ƙoƙon kawunan.

“An samu jimullar ƙoƙon kawunan mutane ashirin da takwas (28) da ƙasusuwa, da ake zargi na waɗanda aka yi garkuwa da su ne,” a cewar Chinaka.

Rundunar ‘yansandan ta ce wasu daga cikin gawarwakin sun riga sun ruɓe, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da asalinsu da kuma yadda suka mutu.

Kawo yanzu dai babu wanda aka kama bisa hannu a aikata wannan ta’asa.

“Ana kan bincike, yayin da aka ci gaba da sa ido a yankin, kuma ana kan ɗaukar matakai domin kama waɗanda ake zargi da aikata wannan laifi,” in ji Chinaka.