Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa jerin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin ke yi tabbas za su haifar da sakamako a gaba.
Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a jawabin da ya gabatar wa al’ummar kasar a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, yayin da kasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Shugaban ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi ba su ne suka durƙusar da tattalin arzikin ƙasar kamar yadda ake zargi. Ya tabbatar da cewa alkawuran da ya yi wa ‘yan Nijeriya sun soma cika.
“Lokacin da wannan gwamnatin ta hau mulki, mun kuduri aniyar gyara abubuwa da dama.
Mun zabi mu cire cutar. Tabbas an sha wahala a sauye-sauyen da suka biyo baya. Illolin sun bayyana. Amma duk da haka, ba za mu taba hada maganin da cutar ba.
“Sauye-sauyen ba su ne suka haifar da rugujewar tattalin arzikinmu ba.
Sun kalubalanci sauye-sauyen. Yanzu, yayin da wasu masu tasiri ke kira da a koma ga tallafin man da ke da tsada kuma ke haifar da matsaloli, dole ne mu yi tsayin daka. Ya kamata mu tuna dalilin da ya sa muka fara wadannan sauye-sauye da kuma irin ci gaban da muka samu zuwa yanzu.
“Bayan shekaru uku da rabi, babu shakka cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya inganta. Tattalin arzikin kasar ya karu da kashi fiye da 4 cikin 100 a bana. Bangaren man fetur da sauran bangarorin da ba na man fetur ba, duk sun taimaka wajen dawo da ci gaba mai dorewa.”
Shugaban ya ce satar man fetur a ƙasashen da ke hako man ta ragu, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ita ma ta ‘‘ragu sosai’’.
‘‘An samu raguwar satar man fetur. Hauhawar farashin kayyayyaki ta rayu sosai raga matakin da ta kai a baya. An kuma sake gina asusun ajiyar ƙudaden waje na Nijeriya.
“Kasuwar musayar kudaden waje ta samu daidaito. A shekarar 2025, Nijeriya ta samu kudaden shiga mafi yawa a tarihinta daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba, inda kudaden suka haura dala biliyan 6. Wannan kudade ne da kamfanonin Nijeriya suka samu ta hanyar kasuwancinsu.”
“Waɗannan ba maganganun da ba su da hujja ba ne. Masu sa ido na ƙasa da ƙasa da ’yan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyin ƙasa da ƙasa suna ganin sauyin da aka samu.
Kowannensu ya fahimci cewa sauye-sauyenmu sun ƙarfafa daidaito da juriyar tattalin arzikin Nijeriya. Kamfanoni masu zaman kansu ma sun dade da tabbatar da hakan, yayin da hannayen jarin ƙasashen waje ke ci gaba da ƙaruwa a kowace shekara.”
Ya jaddada cewa ƙasar ta kai wani muhimmin mataki na samun wadata.
“Lokacin matakan gaggawa ya wuce. Mun gyara tubalin tattalin arzikinmu. Mun samu sauyi a babban aikin da ke gabanmu a yanzu. Tsawon shekaru uku, babban burinmu shi ne gyara tafarkin ƙasar nan.
“Yanzu kuma burinmu a bayyane yake, samar da wadata ga kowa, wadda za ta yadu zuwa ga al’umma baki ɗaya.”

















