Gabas Ta Tsakiya

Pentagon ta ce yaƙin Iran ya laƙume dala biliyan 47

Ƙaruwar kashe kuɗi a fannin soji na barazana ga yiwuwar nasarar Jam’iyyar Republican gabanin zaɓukan rabin wa’adi da za a yi a Amurka a makon gobe.

Newstimehub

Newstimehub

29 Oct, 2026

fb489430 f903 4c82 a703 d3e67f20d00b 1784069828440

Kuɗin masu biyan harajin Amurka da yaƙin Iran ke laƙumewa ya ƙaru zuwa dala biliyan 47.1, in ji wani sabon rahoto da aka gabatar ga majalisar dokokin ƙasar, lamarin da ke ƙara bayyana tasiri na siyasa gabanin zaɓukan rabin wa’adi masu muhimmanci yayin da Shugaba Donald Trump ke duba yiwuwar kai wa Tehran ƙarin hare-hare.

Alƙaluman da Rundunar Tsaro ta Amurka ta tattara, waɗanda suka kasance sahihai zuwa ranar 16 ga watan Oktoba, sun ba da cikakken bayani kan kuɗin da ƙasar ta kashe tun lokacin da aka ƙaddamar da hare-haren sojin tare da Isra’ila a Iran a watan Fabrairu.

Alƙaluman sun nuna ƙaruwar dala biliyan 3.5 na kuɗin da Amurka ke kashewa kan yaƙin tun farkon watan Satumba, a lokacin da kuɗin da ta kashe ya kai kimanin dala biliyan 43.6.

Matsin tattalin arzikin da rikicin ya haddasa da kuma tasirinsa kan kasuwannin makamashi na cikin gida na barazana ga ‘yantakarar jam’iyyar Republican da ke fuskantar masu kaɗa ƙuri’a ranar Talata wajen tabbatar da wanda zai yi rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.

Duk da cewa da farko Trump ya yi alƙawarin shiga yaƙin da zai kai ‘yan makonnin ne kawai, ya bayyana yiwuwar kai sabbin hare-hare bayan zaɓen yayin da yake tura jirgin ruwa mai dakon jiragen yaƙi da kuma dubban dakaru zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Ƙarar da makamai

Karuwar kashe kuɗin ta haifar da adawa a majalisar dokokin ƙasar, inda Fadar White House take neman amincewa ga kasafin kuɗi na tsaron ƙasa da ya kai dala tiriliyan 1.5 tare da dala biliyan 95 da zai tallafa wa ayyukan soji a Gabas Ta Tsakiya.

Maye gurbin makamai na wakiltar kashe kuɗi ɗaya tilo mafi yawa, inda zai laƙume kimanin dala biliyan 29.

Na’urori masu ƙarfi na kakkaɓo makamai—muhimmin tsarin tsaron sama samfurin Patriot da THAAD — su ne suka fi laƙume kuɗaɗe, inda ko wace na’urar kakkaɓo makamai ta Patriot ta kai miliyoyin daloli.

Kuɗin harkokin yaƙi na kai-tsaye sun kai kuɗi dala biliyan 11.9, yayin da na gyara kayayyakin da suka lalace ya kai dala biliyan 6.

Bayanai na hukuma sun bayyana cewa jam’ian sojin Amurka 21 sun mutu—18 daga hare-haren abokan gaba ko faɗuwar jiragen sama ko kuma tura jirage maras matuƙa—kuma 865 sun jikkata, inda rahoton bai ce komai ba game da lalata gine-gine da aka yi a sansanonin soji na yankin.