Manyan bankunan Faransa, BNP Paribas, da na Netherlands, ING, sun ƙara yawan kuɗaɗen da suke bai wa kamfanonin da ake zargi da hannu a take haƙƙin bil’adama da kisan kiyashi a yankunan Falasɗinawa da Isra’ila ta mamaye, a cewar wani rahoto da ƙungiyar haɗin gwiwar Don’t Buy into Occupation (DBIO) ta fitar a ranar Laraba.
Rahoton na shida da ƙungiyar ta fitar, wanda ƙungiyoyi masu zaman kansu 30 daga Falasɗinu da Turai suka bayar da gudummawa wajen tattara shi, ya yi nazari kan alaƙar kuɗi tsakanin cibiyoyin hada-hadar kuɗi 1,096 na Turai da kamfanoni 107 da rahoton ya danganta ayyukansu da take haƙƙoƙi a yankunan Falasɗinawa da Isra’ila ta mamaye.
A cewar rahoton, bankin BNP Paribas ya ƙara yawan kuɗaɗen da yake bai wa wasu kamfanoni, ciki har da kamfanin Amurka da ke kera kayan aikin gine-gine, Caterpillar.
Sojojin Isra’ila sun yi amfani da manyan injinan tono ƙasa na kamfanin Caterpillar wajen rusa gidajen Falasɗinawa da muhimman ababen more rayuwa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
Rahoton ya ce rancen da bankin na Faransa ya bai wa Caterpillar ya tashi daga dala miliyan 721 zuwa miliyan 984, yayin da jarin da ya zuba a kamfanin ya ƙaru daga dala miliyan 275 a shekarar 2025 zuwa miliyan 648 a shekarar 2026.
Shi ma bankin ING na Netherlands ya faɗaɗa hulɗarsa ta kuɗi da kamfanonin da rahoton ya ambata. Bankin ya samar da sabon tsarin bayar da lamuni na dala miliyan 110 ga kamfanin Oshkosh, wanda ke ƙera motocin yaƙi da ake samar wa Ma’aikatar Tsaron Isra’ila.
Binciken ya nuna yadda manyan bankunan Turai ke ci gaba da tallafa wa kamfanonin da ake danganta ayyukansu da hare-haren sojin Isra’ila da mamayar yankunan Falasɗinawa, duk da gargaɗin da ƙungiyoyin fararen hula suka sha yi.
Tsakanin watan Satumban 2024 zuwa Agustan 2026, cibiyoyin kuɗi na Turai sun samar da jimillar dala biliyan 361 ta hanyar bayar da rance da kuma taimaka wa kamfanoni 56 da rahoton ya yi nazari a kansu wajen samun kuɗaɗe.
Rahoton ya kuma ce ya zuwa ranar 15 ga Satumban 2026, masu zuba jari na Turai sun mallaki ko suke kula da hannun jari da takardun lamuni da yawansu ya kai dala tiriliyan 1.745 a kamfanoni 90 daga cikin waɗanda aka ambata.
Jerin kamfanonin ya haɗa da manyan masana’antun kera makamai, kamfanonin fasaha, gine-gine, makamashi da sufuri na ƙasashen duniya.
Daga cikinsu akwai Boeing, Lockheed Martin, RTX, General Dynamics, Caterpillar, Microsoft, Google, Amazon da Palantir Technologies.
















