An kashe Ali Larijani, Sakataren Majalisar Koli ta Tsaro ta Iran, a wani harin sama da Isra’ila ta kai a Tehran, abin da ya kawo ƙarshen doguwar rayuwarsa a siyasa da tsaro. Larijani ya shafe kusan shekaru 40 yana rike da manyan mukamai, tun daga rundunar IRGC har zuwa manyan cibiyoyin yanke shawara a gwamnatin Iran, inda ya zama daya daga cikin manyan masu tsara manufofin kasar.
An haife shi a Najaf a 1957, Larijani ya hada ilimin kimiyyar kwamfuta da falsafa, abin da ya ba shi damar ficewa a harkokin diflomasiyya da siyasa. Ya taba jagorantar gidan talabijin na gwamnati (IRIB), sannan daga bisani ya zama jigo a tattaunawar nukiliya ta Iran, kafin ya zama Shugaban Majalisar Dokoki daga 2008 zuwa 2020, inda aka san shi da iya hada kan bangarori masu sabani.
A shekarun baya-bayan nan, musamman bayan sake naɗa shi a 2025 a matsayin sakataren tsaro, Larijani ya kasance daya daga cikin manyan murya da ke kare matsayar Iran a rikicin da ke kara kamari da Amurka da Isra’ila. Ya kasance mai tsauraran kalamai, yana jaddada cewa Iran ba za ta ja da baya ba idan aka tilasta mata yaki.
Mutuwarsa na zuwa ne a wani lokaci mai matukar muhimmanci, bayan rasuwar tsohon jagoran addini Ali Khamenei da kuma hawa Mojtaba Khamenei kan mulki. Masu sharhi na ganin rashin Larijani zai bar babban gibi a cikin tsarin jagoranci da shawara a Iran yayin da yankin ke fuskantar barazanar babbar fada.














