A wani sabon mataki da ya tayar da hankula a fagen siyasar duniya, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa ta kaddamar da gagarumin farmaki a Venezuela, wanda ya kai ga kama Shugaba Nicolas Maduro tare da matarsa sannan aka fitar da su daga ƙasar.
Trump ya bayyana hakan ne ta wata sanarwa da aka wallafa a Truth Social, inda ya ce aikin ya gudana cikin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da na aiwatar da doka na Amurka.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin nasara ga abin da ya kira ceto al’ummar Venezuela daga gwamnatin Maduro. Wannan labari na ci gaba, kuma ana sa ran karin bayani a nan gaba yayin da ake jiran martanin hukumomin Venezuela da ƙarin haske kan halin da ake ciki.
Majiyar Labari: TRT WORLD














