Hukumomin Bahrain sun sanar da sake jin ƙararrawar gaggawa karo na biyu cikin awanni huɗu, inda suka buƙaci mazauna ƙasar su kwantar da hankula tare da garzayawa zuwa wuraren tsaro mafi kusa. Ba a bayar da cikakken bayani kan dalilin ƙararrawar ba a hukumance.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke ƙara tsananta, musamman bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ke kaiwa kan ƙasashen Gulf da ke ɗauke da sansanonin sojin Amurka. Bahrain na daga cikin ƙasashen da suka fi fuskantar irin waɗannan hare-hare tun bayan farmakin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.
Rahotanni sun nuna cewa wasu hare-hare sun taɓa cibiyoyi da ke da alaƙa da rundunar sojin ruwan Amurka ta Fifth Fleet a Bahrain. Wannan ya ƙara jefa fargaba a tsakanin jama’a yayin da ake ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.
Yayin da bangarorin ke ci gaba da musayar hare-hare, ana fargabar cewa rikicin zai kara bazuwa a yankin, wanda ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasashen Gulf baki daya.
Majiyar Labari: AA














