Umarnin zama-gida da ƙungiyar ‘yan aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB) ta haramta a yankin kudu maso gabashin Najeriya ya haifar da mutuwar mutane fiye da 700 a cikin shekaru huɗu da suka gabata, kamar yadda wani rahoto daga wata cibiyar bincike ya bayyana.
IPOB, wadda ke fafutukar ɓallewa daga Nijeriya don kafa ƙasa mai zaman kanta a yankin kudu maso gabas da kabilar Igbo suka fi yawa, an ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci daga hukumomin Nijeriya.
Rahoton na SBM Intelligence ya bayyana cewa mace-macen sun faru ne sakamakon kashe fararen hula da suka ƙi bin umarnin zama-gida a kowace Litinin da wasu ranaku na musamman, da kuma rikici tsakanin IPOB da jami’an tsaron Nijeriya.
“Hanyoyin tilasta bin umarnin IPOB, ciki har da ƙona gidajecda fashi da makami, da kisan kai na musamman, sun haifar da yanayin tsoro,” in ji rahoton SBM.
Bin umarni cikin tsoro
“Duk da cewa akwai yawan bin umarnin zaman-gida a shekarar 2021 (82.61%), bincike ya nuna cewa goyon baya na gaske ya ragu zuwa (29%) yanzu, inda mutane da dama ke bin umarnin cikin tsoro.”
Wani mai magana da yawun IPOB ya musanta cewa ƙungiyar ce ke da alhakin kashe-kashen.
“Wadanda ke haifar da kashe-kashen su ne masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda da gwamnati ta ɗauka don ɓata sunan IPOB,” in ji mai magana da yawun ƙungiyar.
Gwamnati ba ta yi wani tsokaci kan rahoton ko ikirarin IPOB ba.
IPOB ta fara zanga-zangar zaman-gida a watan Agustan 2021 a jihohi biyar na kudu maso gabashin Nijeriya, tana amfani da wannan matakin don neman a saki shugabanta, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar shari’a a babban birnin tarayya Abuja kan zarge-zargen ta’addanci.
Ƙungiyar ta dakatar da zanga-zangar mako-mako bayan wasu kwanaki, tana mai cewa hakan ya biyo bayan “umarnin kai tsaye” daga Kanu, wanda ke tsare tun daga shekarar 2021, kuma ta sake dawo da shi ne kawai a ranakun da za a gurfanar da shi a kotu.
Rikicin ƙungiyoyi
Duk da haka, wasu ƙungiyoyin da ke ikirarin biyayya ga IPOB da kuma rassa a cikin ƙungiyar sun ci gaba da tilasta umarnin zanga-zangar mako-mako, suna kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati da kuma mutanen da ake ganin suna goyon bayan gwamnati.
‘Yan sanda sun zargi IPOB da hannu a wasu abubuwa, ciki har da harin da aka kai wa gidan yari a shekarar 2021 da kuma kisan matafiya sama da 30 a farkon wannan watan.
IPOB ta musanta cewa tana da hannu a waɗannan hare-haren guda biyu.
Rahoton SBM ya ƙara da cewa, ban da mutuwar da aka samu, umarnin zaman-gida wanda ke dakatar da harkokin tattalin arziki a kudu maso gabas a kowanne Litinin da kuma ranakun da Kanu ke bayyana a kotu, ya haifar da asarar tattalin arziki da ta haura naira tiriliyan 7.6 ($4.79 biliyan).
Wata fafutukar mai kama da wannan da aka taɓa yi a yankin ya jefa Nijeriya cikin yaƙin basasa a shekarun 1960, inda fiye da mutum miliyan ɗaya suka rasa rayukansu.