Turkiyya

Ana buƙatar haɗin kai mai ƙarfi domin farfaɗo da kasuwancin duniya: Erdogan

A jawabin da ya gabatar a taron shugabannin G20 a Johannesburg da ke Afirka ta Kudu a ranar Asabar, shugaban ya bayyana goyon bayan Ankara wajen karɓar wata hanya da ta dogara ga adalci da daidaito domin sake tsarin bayar da bashi, musamman ga kasa

Newstimehub

Newstimehub

22 Nov, 2025

8a8e1bd50597a57641d54d226ecd26969db4f59b70b5fad64a77ab17827db26f

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ana bukatar haɗin kai sosai na ƙasa da ƙasa, sabbin manufofi da kuma ɗorewar hanyoyin jigilar kayayyakin domin farfado da kasuwancin duniya.

A jawabin da ya gabatar a taron shugabannin G20 a Johannesburg da ke Afirka ta Kudu a ranar Asabar, shugaban ya bayyana goyon bayan Ankara wajen karɓar wata hanya da ta dogara ga adalci da daidaito domin sake tsarin bayar da bashi, musamman ga kasashen da ke da ƙarancin kuɗaɗen shiga.

“Ina gayyatar dukkan G20 su ɗauki ƙarin nauyi wajen gina tattalin arzikin duniya wanda ya haɗa kowa, ba a bar kowa a baya ba,” in ji Erdogan.

Shugaban Turkiyya yana Johannesburg don wannan taro na kwanaki biyu wanda ya fara a ranar Asabar kuma yake mai mayar da hankali kan magance wasu daga cikin manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.