Turkiyya

China ta yaba wa Turkiyya, Saudiyya, Qatar kan rawa a tsagaita wuta tsakanin Pakistan da Afghnistan

Beijin ta ya kira ga Islamabad da Kabul su ‘koma tattaunawar zaman lafiya ba tare da ɓata lokaci ba, su yi aiki don samar da tsagaita wuta gamsasshe mai dorewa’ don wanzar da zaman lafiya a yankin.

Newstimehub

Newstimehub

19 Mar, 2026

2026 02 27t103207z 2004455345 rc2aujajxx8s rtrmadp 3 afghanistan pakistan

A ranar Alhamis, China ta yaba wa rawar da Turkiyya, da Saudiyya da Qatar suka taka wajen cim ma tsagaita wuta tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Yayin da ta yi maraba da sanarwar tsagaita wutar da Islamabad da Kabul suka yi, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta China, Lin Jian, ya ce Beijing na fatan cewa ƙasashen biyu “za su zauna cikin natsuwa, su taka-tsan-tsana, su koma tattaunawar zaman lafiya ba tare da ɓata lokaci ba, su tabbatar da cikakken dawwamammen tsagaita wuta cikin kankanin lokaci, su magance bambance-bambancen da ke tsakannsu da rikice-rikice ta hanyar tattaunawa yadda ya kamata, kuma su yi aiki tare don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin kasashen biyu da yankin.”

“China na yabawa kokarin da wasu ƙasashen Musulunci suka taka,” in ji Lin, yana nuni da rawar da Ankara, Riyadh da Doha suka taka wajen cim ma tsagaita wutar.

Ya ce China tana shiga tsakani tsakanin ɓangarorin ta hanyoyinta, kuma tana shirye ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata wajen cim ma wannan yunƙuri.

A ranar Laraba Pakistan ta ce ta dakatar da “ayyukan sojojinta” na “ɗan wani lokaci” saboda bukukuwan sallah na Musulmai, bayan buƙatun Turkiyya, da Saudiyya da Qatar.

Dakatarwar ta ɗan wani lokaci

Daga baya, kakakin gwamnatin Afghanistan, Zabihullah Mujahid, ya sanar da dakatar da ayyukan ƙasarsa na yaƙi na ɗan lokaci gabanin idin Ƙaramar Sallah, yana mai danganta hakan ga kyakkyawar niyya da kuma buƙatun Saudiyya, da Turkiyya da Qatar.

Dangantaka tsakanin Afghanistan da Pakistan ta taɓarɓare a ‘yan makonnin nan yayin da tashin hankali a kan iyaka ya ƙaru, wanda ya janyo asarar rayuka da lalata dukiya.

Tun ƙarshen Fabrairu, arangama a iyaka ta yi ajalin akalla mutane 107 a ɓangarorin biyu, ciki har da sojoji 13 da fararen hula 5 a Pakistan, yayin da wani soja har yanzu ba a same shi ba.

Hukumomin Afghanistan sun bayar da rahoton cewa sojoji 13 da fararen hula 76 sun mutu a Afghanistan, ba tare da lissafa sabbin asarar rayuka daga harin da aka kai wani asibitin ba a ranar Litinin, inda jami’an Afghanistan ke iƙirarin cewa harin sama na Pakistan ya kashe mutane 408.

Ofishin da ke taimaka wa Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya ba da rahoton mutuwar fararen hula 76 da raunuka 213 a Afghanistan tsakanin 26 Fabrairu da 16 Maris, ba tare da haɗawa da harin na ranar Litinin ba.

Islamabad na zargin Afghanistan da bai wa ƙungiyoyin ‘yanta’adda masu adawa da Pakistan mafaka, abin da Kabul ke musantawa.