Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da hakkin dan Adam a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ya bayyana matukar damuwa kan yadda ake amfani da fyade a matsayin makamin yaki a rikicin da ke gudana a kasar. Rahoton da aka fitar a Kinshasa ya nuna cewa a shekarar 2025 an rubuta akalla laifukan cin zarafin jima’i 887 da suka shafi mutane 1,534, mafi yawansu mata da ‘yan mata.
Rahoton ya ce yankin gabashin Congo, musamman lardunan North Kivu da South Kivu, su ne wuraren da aka fi samun irin wadannan laifuka, inda kusan kashi 80 cikin 100 na wadanda abin ya shafa suka fito daga wadannan yankuna. Yawancin laifukan dai kungiyoyin ‘yan bindiga ne suka aikata, ciki har da kungiyar M23, Wazalendo, CODECO, Maï-Maï da kuma ‘yan tawayen ADF da FDLR.
Majalisar Dinkin Duniya ta kuma nuna damuwa kan bautar jima’i, inda ake tsare mata da ‘yan mata tare da tilasta musu fyade sau da dama da kuma daukar ciki. Yaran da ake haifa sakamakon wannan tashin hankali kan fuskanci wariya daga al’umma da iyalai, lamarin da ke kara jefa su cikin hadari.
Kungiyar ta bukaci hukumomin Congo su gaggauta hukunta wadanda ke da alhakin wadannan laifuka tare da kara tallafi ga wadanda abin ya shafa, domin a yanzu kasa da kashi 2 cikin 100 na wadanda aka cutar ne ke samun cikakken tallafin jinya, shawarwari da kuma taimakon shari’a.














