Nijeriya

ECOWAS za ta kafa runduna mai dakaru 260,000 don yaƙar ta’addanci

Shugaba hukumar ƙungiyar ECOWAS, Omar Alieu Touray, ne ya bayyana wannan a taron manyan hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka  na shekarar 2025 a Abuja.

Newstimehub

Newstimehub

26 Aug, 2025

493230144 1244680070354318 7267580156167756196 n

Ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce tana shirin kafa runduna mai dakaru 260,000 domin yaƙar ta’addanci.

Shugaba hukumar ƙungiyar ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana hanan a taron manyan hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka  na shekarar 2025 a Abuja.

Jigon taron shi ne “Yaƙi da barazana ga zaman lafiya da tsaron Afirka na wannan zamanin: muhimmancin dabarun haɗin kai na tsaro.”

Touray, wanda ya samu wakilcin kwamishina mai kula da harkar siyasa da zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce wannan wani ɓangare ne na rage tushen ta’addanci da sauran na’o’i na rashin tsaro a yankin.