Dan wasan tsakiya na Senegal, Idrissa Gueye, ya ce tawagarsu ta cancanci lashe kofin AFCON duk da cewa CAF ta bai wa Morocco nasara bayan sauya sakamakon wasan karshe. Senegal ta ci Morocco 1-0 a karin lokaci, amma daga baya an juya sakamakon zuwa 3-0 ga Morocco saboda zargin ficewar ’yan wasan Senegal daga fili na tsawon mintuna 15.
Gueye ya bayyana cewa a shirye yake ya mayar da lambobin yabo idan hakan zai rage tashin hankali tsakanin kasashen biyu, duk da cewa ya dage cewa Senegal ce ta yi nasara a fili. Ya ce nasara a kwallon kafa ana samun ta ne a fili, ba a ofisoshi ba, yana mai jaddada cewa su ne zakarun Afirka a ra’ayinsu.
Sai dai ya nuna rashin jin dadinsa da matakin hukumar kwallon kafar Senegal na daukaka kara zuwa kotun CAS, yana mai cewa da shi ne da ba zai shigar da kara ba. A cewarsa, lamarin ya wuce kima kuma ya kamata a duba shi ta fuskar wasanni ba siyasa ba.
Wasan karshe ya rikice ne bayan Morocco ta samu bugun fanareti mai cece-kuce a karshen wasa, wanda ya sa ’yan wasan Senegal suka fice daga fili na wani lokaci. Bayan dawowa wasan, Morocco ta kasa cin kwallo daga fanareti, inda Senegal ta ci kwallo a karin lokaci ta hannun Pape Gueye.














