Gwamnatin Nijeriya ta fara kwashe ‘yan kasarta daga Iran sakamakon rikicin da ke kara tsananta tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila. Shugabar Hukumar ‘Yan Nijeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce jami’an ofishin jakadancin Nijeriya na raka ‘yan kasar da ke son barin Iran zuwa kan iyakar Armenia domin su tsallaka cikin aminci.
A cewarta, jami’an Nijeriya na jiran ‘yan kasar a kan iyaka domin tarbar su, tare da taimaka musu su koma gida lafiya. Ta kuma tabbatar da cewa ba a samu rahoton mutuwar wani dan Nijeriya ba sakamakon rikicin da ke gudana a Iran.
Matakin kwashe ‘yan Nijeriyar na zuwa ne yayin da rikicin da ya barke kwanaki goma sha daya da suka wuce ya riga ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 1,300 a Iran, yayin da dubban wasu suka jikkata ko suka rasa muhallansu.














