Duniya

096cff67ae1149b59857127c1d2f6071cec757fff15c584aec75776668d3799d

China ta zartar da hukuncin kisa kan tsohon ma’aikacin banki kan karɓar cin hancin dala miliyan 156

An samu Bai Tianhui, babban jami’i na kamfanin China Huarong International Holdings (CHIH), da laifin karbar kudi fiye da dala miliyan 156 a lokacin da yake ba da gyaran abubuwa a cikin sarrafa da kuma samarwa na ayyuka tsakanin 2014 da 2018.

Venezuela ta rantsar sabbin sojoji 5,600 yayin da rikici tsakaninta da Amurka ke ƙara tsami

Gwamnatin Venezuela ta bayyana ‘‘barazanar mulkin mallaka’’ da kuma ayyukan sojojin Amurka na baya-bayan nan a yankin Caribbean a matsayin dalilanta na fadada rundunonin sojin ƙasar.

Ziyarar Putin zuwa India yayin ƙoƙarin kawo zaman lafiya a Ukraine

Ziyarar Putin tana nuna cewa India da Rasha na ƙoƙarin ƙarfafa hulɗarsu duk da matsin lamba, yayin da kowanne bangare ke neman ci gaba ba tare da rasa muhimman kawaye ba.

Amurka, Rasha da China na ƙara matsa lamba domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

Tattaunawar diplomasiya na ƙaruwa amma manyan sabani tsakanin kasashen na ci gaba da hana a samu matsaya guda.

Afirka

31188d8ca138d9d09be7bb5748535a031eee599bce2bd4f6eff3c49cfdda5561

Mutum fiye da 1,000 sun tsere daga Kordofan na Sudan cikin kwana biyu yayin da yaƙi ya ƙazanta: IOM

Tserewar da mutane suke ci gaba da yi na faruwa ne a yayin da gumurzu ke ƙara yin ƙamari tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF.

Ghana ta yi tur da “wulaƙanta” ‘yan ƙasarta da Isra’ila ta yi a filin jirgin sama na Tel Aviv

Ghana ta ce an tsare matafiya bakwai ‘yan Ghana ba tare da wani dalili ba bayan isarsu Tel Aviv ranar Lahadi. Daga cikinsu akwai mambobi hudu na tawagar ‘yanmajalisa da suka halarci taron shekara-shekara na tsaron intanet na kasa da kasa.

Dukkan mutanen da ke ciki jirgin sojoji na Sudan sun mutu a hatsarin da ya yi

Daga cikin mamatan akwai matukin jirgi na soja Omran Mirghani, in ji ɗan’uwansa, shahararren ɗanjarida na Sudan Osman Mirghani, wanda ya nuna alhininsa a shafukan sada zumunta.

ECOWAS ta ayyana dokar ta-ɓaci a Yammacin Afirka kan ‘rashin zaman lafiya’ na siyasa da tsaro

Sanarwar ECOWAS na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da sojoji suka yi a ƙarshen makon jiya a Jamhuriyar Benin, wanda ya biyo bayan wani juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau.