Nijeriya

Hare-haren ƙunar-baƙin-wake sun kashe mutum aƙalla 23 a birnin Maiduguri na Nijeriya: Hukumomi

An kai hare-haren ne a ƙofar shiga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da Monday Market da kuma gidan waya da ke birnin.

Newstimehub

Newstimehub

17 Mar, 2026

2026 03 17t052844z 1 lynxmpem2g07m rtroptp 3 nigeria security

Mutum aƙalla 23 ne suka mutu yayin da mutum 146 suka jikkata a hare-haren ƙunar-baƙin-wake a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya ranar Litinin da dare, a cewar hukumomi.

Bamabaman sun tashi ne a ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da Monday Market da kuma gidan wayan da ke birnin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar Borno ASP Nahum Kenneth Daso ya ce ana tunanin hare-haren ƙunar-baƙin-wake suka haddasa tashin bama-baman.

Sai dai ya ce abubuwa sun koma yadda ake a da a wuraren, yana mai kira ga mutane su bai wa ‘yansanda rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Surajo Abdullahi, shugaban yanki na hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ya tabbatar mata cewa mutum aƙalla 23 ne suka mutu sannan mutum 169 suka jikkata a hare-haren.

“A halin yanzu mutum 108 suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, kuma 20 suna Asibitin Tunawa da Umaru Shehu yayin da mutum 17 ke Asibitin Ƙwararru na Maiduguri,” in ji shi .

Mazauna Maiduguri da yawa dai sun ce cikin ‘yan shekarunan birnin ya fara mantawa da hare-haren bamabamai da harbe-harbe amma a baya bayan nan ana lamura sun soma dagulewa.