Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce Mashigar Hormuz a buɗe take, amma jiragen ruwa suna fargabar wucewa saboda tasirin yaƙin da Amurka da Isra’ila suke yi da Tehran. Ya bayyana cewa matsalar ba rufewar mashigar ba ce, sai dai tsoron kamfanonin inshora da ke kauce wa haɗarin yaƙi.
A cikin saƙonsa a shafin X, Araghchi ya jaddada cewa babu wani kamfanin inshora ko ɗan Iran da zai tsorata da barazanar waje, yana mai kira da a mutunta ’yancin zirga-zirga da kuma ciniki a teku.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ma ta sake tabbatar da cewa mashigar ba a rufe take ba, amma ta yi gargadin cewa jiragen ruwa na bangarorin da ke yakar Iran ba za su wuce cikin sauƙi ba.
Tun farkon watan Maris, an samu tangarda a mashigar Hormuz — wata muhimmiyar hanya ta jigilar mai da gas a duniya — lamarin da ya jawo tashin farashin kaya da makamashi. Wannan ya kara matsin lamba ga tattalin arzikin duniya, musamman ganin yadda mashigar ke daukar kaso mai yawa na cinikin makamashi.
A gefe guda, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari kan muhimman cibiyoyin Iran idan ba a bude mashigar ba cikin gaggawa. Rikicin yankin ya kara tsananta tun bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka fara, inda Iran ta mayar da martani da hare-haren drones da makamai masu linzami a yankin.














