Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa an kashe Ali Larijani da kwamandan dakarun Basij, Gholamreza Soleimani, a wasu hare-hare ta sama da aka kai da daddare, sai dai hukumomin Iran ba su tabbatar da hakan ba.
A ranar Talata ne Ministan Tsaron Isra’ila Israel Katz ya yi ikirarin cewa babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, ya mutu a wani hari ta sama.
A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, Katz ya yi ikirarin cewa an “kawar” da Larijani da kwamandan Basij, Gholamreza Soleimani, a hare-haren da aka kai cikin dare.
“Yanzu ne Babban Hafsan Soji ya sanar da ni cewa an kawar da Larijani, Sakataren Majalisar Koli ta Tsaro ta Kasa, da kuma shugaban dakarun Basij — wanda shi ne babban rukunin danniya na Iran — (Soleimani), a daren jiya,” in ji Katz a cikin sanarwar da ma’aikatarsa ta fitar.
Tun da farko kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa Larijani, shugaban Majalisar Koli ta Tsaro ta Iran, shi ne dalilin hare-haren da Isra’ila ta kai da daddare.
Har yanzu dai babu wani martani daga hukumomin Iran dangane da wannan ikirari.
Sai dai, bayan ikirarin na Isra’ila, kafofin yada labaran gwamnatin Iran sun wallafa wani rubutu na hannu da aka ce na Larijani ne, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Sako na karshe a shafin X na Larijani an wallafa shi ne da misalin karfe 09:40 na safe (agogon GMT) a ranar Talata, 17 ga watan Maris. Sakon wani rubutu ne da hannu da ke jinjina wa wadanda suka rasa rayukansu a rundunar sojin ruwan Iran a lokacin jana’izarsu.
Idan har aka tabbatar da mutuwarsa, zai kasance babban jami’in Iran mafi girma da aka kashe bayan Jagora Ali Khamenei, wanda ya rasu a ranar farko ta yakin.
Larijani, tsohon mai tattaunawa kan batun makamin nukiliya kuma na hannun damar Khamenei, an gan shi a birnin Tehran ranar Juma’a yana halartar jerin gwanon ranar Kudus.
Daga baya a ranar, Amurka ta sanar da ba da ladan dalar Amurka miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga manyan jami’an soja da na leken asiri na Iran, ciki har da Larijani, a matsayin daya daga cikin mutane 10 da ke da alaka da dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC).














