Kasashe sun yi alkawarin $170 ga WHO gabanin ficewar Amurka

China da Qatar da Switzerland da wasu kasashen sun yi alkawarin dala miliyan 170 ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Newstimehub

Newstimehub

21 May, 2025

2025 05 20t123250z 1587169285 rc2nlea92z0d rtrmadp 3 health who pandemic agreement 1 scaled

Ƙasashen China da Qatar da Switzerland da sauransu sun yi alƙawarin bayar da sama da dala miliyan 170 ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a taronta na ranar Talata.

Har ila yau, ƙasashen sun amince da ƙarin kuɗaɗen don taimakawa wajen rage giɓin da ake sa ran za a samu na babbar mai bayar da agajin, Amurka.

“Ina godiya ga kowace ƙasa mamba da abokan hulɗar da suka yi alƙawarin bayar da agaji,” in ji Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban daraktan hukumar ta WHO a cikin wata sanarwa.

Ya ƙara da cewa: “A cikin yanayi mai wahala ga lafiyar duniya, waɗannan kuɗaɗe za su taimaka mana wajen adanawa da kuma faɗaɗa ayyukanmu na ceton rai.”