‘Yan sanda biyu sun yi shahada yayin da wasu biyun suka jikkata a wani harin bindiga da aka kai kan wani caji ofis a lardin Izmir da ke yammacin Turkiyya a ranar Litinin, inda aka kama wani matashi ɗan shekara 16, in ji jami’ai.
Matashin ya bude wuta da bindiga a caji ofis ɗin Salih İsgoren da ke yankin Balcova na Izmir.
Ministan Cikin Gida, Ali Yerlikaya ya bayyana wannan hari a matsayin “mugun abu,” inda ya ce ya yi sanadiyyar shahadar ‘yan sanda biyu, yayin da wani ya samu “mummunan rauni” kuma wani ya samu “rauni kaɗan.”
“Wanda ake zargi a wannan al’amari, matashi ne mai shekara 16 mai suna E.B., an kama shi kuma an ƙaddamar da bincike,” Yerlikaya ya rubuta a shafin X.
An kai jami’in da ya jikkata zuwa Asibitin Bincike da Aiwatarwa na Jami’ar Dokuz Eylul.














