Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce za su taƙaita inda ‘yan wasu ƙasashen Turai za su iya samun bizar shiga ƙasar da ke yankin Sahel, sakamakon matsala da su ma ‘yan Nijar ke fuskanta wajen samun bizar shiga Turai daga ofisoshin jakadancin ƙasashen.
Hakan na zuwa ne bayan da Ministan Harkokin Wajen ƙasar Bakary Yaou Sangare ya koka kan yadda ‘yan Nijar ke ci gaba da tafiya zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da ƙasar domin kammala ƙa’idojin samun biza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Ministan ya ce Nijar ta gabatar da buƙatar a bai wa ofisoshin jakadancin Turai da ke Yamai izinin ba da biza a wurin, wanda a cewarsa, “ba a samu amsa ba kawo yanzu”.
“Daga yanzu ofisoshin jakadancin Nijar a Geneva da Ankara da Moscow ne kaɗai ke da izinin ba da bizar shiga Nijar ga ‘yan ƙasashe kamar: Italiya, da Netherlands, da Tarayyar Jamus, da Masarautar Belgium, da kuma Birtaniya,” in ji Ministan.
‘Ƙa’idar mayar da martani’














