Kashim Shettima ya gana da Sakatare-Janar na MDD kan yunkurin Nijeriya na neman kujerar dindindin

Tattaunawar ta kuma shafi sauyin yanayi, da ci gaba mai ɗorewa, da haɗin gwiwar Nijeriya da shirin raya ƙasa na Majalisar Dinkin Duniya.
26 Sep, 2025
Sojojin Nijeriya sun kama masu aikata laifuka fiye da 120 ciki har da masu taimaka w ‘yan ta’adda 26

A arewa maso gabashin Nijeriya, dakarun Operation Hadin Kai sun kuɓutar da mutum uku da aka yi garkuwa da su kuma suka kama masu taimaka wa ‘yan ta’adda 26 tare da kashe mayaƙan Boko Haram a Jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
26 Sep, 2025
An yanke wa Sojojin Nijeriya uku hukuncin ɗaurin rai da rai

An yanke wa sojojin hukuncin laifuka da dama, wadanda suka hada da sata, da yin mu’amala da harsasai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma taimaka wa ‘yan ta’adda wadanda duk hukuncinsu ke karkashin dokar kotun sojin Nijeriya
25 Sep, 2025
Tsananin gudu da kura-kuran matuƙi ne suka janyo faduwar jirgin kasan Abuja-Kaduna – NRC

Shugaban hukumar ya yi alkawarin cewa za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin bincike ya gabatar.
25 Sep, 2025

UNGA 80: Abubuwa biyar da Kashim Shettima ya faɗa a zauren MDD

Gwamnatin Nijeriya ta damu kan bidiyon tallan bogi na Tinubu da aka yi da Ƙirƙirarriyar Basira

CBN ya ƙaddamar da kamfe kan cewa masu wulaƙanta Naira za su iya fuskantar ɗauri

An gano ƙarin gawarwakin ‘yan sandan Nijeriya da ‘yan bindiga suka kashe a Benue

Majalisar Wakilan Nijeriya ta ce tana tare da Tinubu ɗari bisa ɗari domin ciwo wa Nijeriya bashi
24 Sep, 2025
Yadda ‘yan wasu Nijeriya suka yi kashin ƙulli 116 na heroin da hodar ibilis a gaban jami’an NDLEA
Mutumin da ake zargi da safarar hodar ibilis ya ce ya shafe fiye da awa biyu yana ƙoƙarin tura ɗauri tara na hodar ibilis a cikin duburarsa.

24 Sep, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta ƙwace lasisin kamfanonin haƙar ma’adinai 1,263
A jimilla, gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta ƙwace lasisin haƙar ma’adinai 3, 794 ciki har da lasisi 619 da aka ƙwace domin gaza biyan haraji na shekara-shekara da kuma 912 da aka ƙwace saboda rashin aiki da su.

24 Sep, 2025
Sassa daban-daban na Jihar Kaduna na cikin duhu sakamakon faɗuwar turken dakon lantarki
Faɗuwar ta faru ne sakamakon ruwan sama mai yawa da iska mai karfi, inda kuma ayyukan masu lalata turakun suka bayar da gudunmawa, inda aka gano cewa an cire muhimman sassan turken.

24 Sep, 2025
Obasanjo ya musanta neman wa’adi na uku, ya ce da ya ga dama da ya samu
“Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar.

24 Sep, 2025
Za a ba da tukwuicin N10m don kama mutanen da suka kashe limamin Cocin Katolika a Enugu ta Nijeriya
Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka.

24 Sep, 2025
Boko Haram: Sojojin Saman Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 25 a Borno da Yobe
Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jiragen yaƙinsu sun kai samamen ne ranar 18 ga watan Satumba bayan sun samu bayanan sirri daga sojojin ƙasa.

24 Sep, 2025
Dubban ‘yan Nijeriya sun tsere zuwa Kamaru bayan harin ‘yan ta’adda a Jihar Borno
‘Yan ta’addan sun kai hari garuruwa biyu a Jihar Borno waɗanda ke a kusa da iyakar Kamaru, lamarin da ya tilasta wa kimanin fararen hula 5,000 tserewa zuwa ƙasar ta Kamaru.

24 Sep, 2025
An dakatar da shugabannin makarantun sakandare shida daga aiki a Sokoto
Kwamishinan ya kuma ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani jami’in da aka samu da laifi.

24 Sep, 2025
Jihar Ogun ta Nijeriya ta rufe kamfanonin ‘yan China biyar kan tsangwamar jami’an gwamnati
Wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta ce matsalar ta soma ne a lokacin da tawagar hukumar ta tabbatar da bin dokar ta isa harabar kamfanonin ranar Laraba, kuma ma’aikata suka kai musu farmaki.

18 Sep, 2025
Ma’aikatan FIRS huɗu da na UCP 6 sun rasa rayukansu a gobarar wani babban ofis a Legas
Bidiyon da aka dauka a wajen ya nuna yadda mazauna ofis din ke tsalle suna fadowa saboda tsoro, inda masu kallo ke kai agaji da tsani da katifu don taimaka musu.



