Saudiyya ta saki ‘yan Nijeriya uku da ta tsare bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Daraktan yada labarai da yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa sakin nasu ya biyo bayan wata yarjejeniya tsakanin hukumar ta NDLEA da gwamnatin Saudiyya.
17 Sep, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta kai ƙarar Sowore da Meta da X kotu kan cin fuskar Tinubu

Lauyoyin Sowore sun ƙara da cewa dole Meta da X su gane cewa a muddin suka yi biyayya ga buƙatar gwamnatin Nijeriya ta hana tofa albarcin baki, to sun saɓa wa doka kuma sun zama masu hannu a laifin danne gwagwarmayar samun ‘yanci.
17 Sep, 2025
Yayin da ake yarjejeniyar zaman lafiya a Katsina: ‘Yan ta’adda sun sace mutum 55 a Zamfara

Wasu masana na ganin idan ana so a magance matsalar tsaro a arewa maso yammacin Nijeriya, ya kamata gwamnatoci su yi sulhu da ‘yan bindiga a yankin, yayin da wasu ke ganin sulhu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba.
17 Sep, 2025
Hauhawar farashi a Nijeriya ta ragu karo na biyar a jere – NBS

Alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa hauhawar farashin ta ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 daga kashi 21.88 cikin 100 da ta kasance a watan Yuli.
16 Sep, 2025

Motocin Dangote na CNG sun fara lodin mai a matatarsa don yin dakonsa kyauta a faɗin Nijeriya

Mutum 19 ‘yan ɗaukar amarya sun rasu bayan motarsu ta faɗa cikin kogi a Zamfara

Gwamnatin Jihar Kano ta goyi bayan ƙudurin haramta auren jinsi

Likitoci masu neman ƙwarewa sun tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya

Babu gudu babu ja da baya kan dakon mai kyauta a Nijeriya— Matatar Dangote
12 Sep, 2025
Kotun Nijeriya ta ɗaure shugaban ƙungiyar Ansaru shekara 15 kan ta’addanci
Mahmud Usman ya amsa laifin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba inda yake amfani da kuɗinsu wajen sayen makamai domin kai hare-haren ta’addanci da yin garkuwa da mutane.

11 Sep, 2025
Mele Kyari: EFCC ta yi wa tsohon shugaban NNPCL tambayoyi
EFCC tana bincike ne kan yadda aka kashe kimanin dala biliyan biyu a gyaran matatun mai na Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari.

11 Sep, 2025
Ghana ta karɓi ‘yan Nijeriya da aka kora daga Amurka – Mahama
Yawancinsu ‘yan Nijeriya ne, yayin da ɗaya daga cikinsu ya kasance ɗan ƙasar Gambiya.

10 Sep, 2025
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da Kwamitin Shura kan harkokin addini da zamantakewa
Majalisar ta ƙunshi mambobi 67 waɗanda aka zaɓo daga faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

10 Sep, 2025
NUPENG ta dakatar da yajin aikinta bayan ta ƙulla yarjejeniya da matatar mai ta Dangote
An cim ma yarjejeniyar a wata tattaunawa ta sirri da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kira kuma ministan kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC) suka halarta.

10 Sep, 2025
An haramta amfani da kwale-kwale marasa lasisi a Nijeriya domin inganta tsaro da kare rayuka
Matakin hakan na zuwa ne biyo bayan wasu munanan haɗurran kwale-kwalen ruwa da suka yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama a ‘yan watannin baya-bayan nan a Nijeriya.

9 Sep, 2025
Ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya na sulhunta NUPENG da Dangote ya ci tura
Ƙungiyar NUPENG ta yi shelar cewa za ta fara yajin aiki daga ranar Litinin, 8 ga watan Satumbar shekarar 2025, kan zargin da ta yi wa kamfanin Dangote cewa yana ɗaukar matakan da suka saɓa wa dokokin ƙwadago.

8 Sep, 2025
Gwamnatin Nijeriya tana yunƙurin kammala tsarin Manufofin Iyali na Ƙasa
Gwamnatin Nijeriya na ƙoƙarin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na Ƙasa wato (National Family Policy) don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar.

8 Sep, 2025
Dalilan NUPENG na yin yajin aiki a kan Matatar Dangote
Shugaban ƙungiyar NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana ranar Lahadi cewa ƙungiyar za ta ci gaba da yajin aikin zuwa ƙarshen tattaunawar ƙungiyar da gwamnati ranar Litinin.

7 Sep, 2025
Dar-El-Jamal: ‘Yan Boko Haram sun kashe mutum 63 a Jihar Borno a Nijeriya
An kai harin ne ranar Juma’a da daddare a garin Darul Jamal, wanda ke da sansanin soji a kan iyakar Nijeriya da Kamaru.



