Sassa daban-daban na Jihar Kaduna na cikin duhu sakamakon faɗuwar turken dakon lantarki

Faɗuwar ta faru ne sakamakon ruwan sama mai yawa da iska mai karfi, inda kuma ayyukan masu lalata turakun suka bayar da gudunmawa, inda aka gano cewa an cire muhimman sassan turken.
24 Sep, 2025
Obasanjo ya musanta neman wa’adi na uku, ya ce da ya ga dama da ya samu

“Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar.
24 Sep, 2025
Za a ba da tukwuicin N10m don kama mutanen da suka kashe limamin Cocin Katolika a Enugu ta Nijeriya

Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka.
24 Sep, 2025
Boko Haram: Sojojin Saman Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 25 a Borno da Yobe

Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jiragen yaƙinsu sun kai samamen ne ranar 18 ga watan Satumba bayan sun samu bayanan sirri daga sojojin ƙasa.
24 Sep, 2025

Dubban ‘yan Nijeriya sun tsere zuwa Kamaru bayan harin ‘yan ta’adda a Jihar Borno

An dakatar da shugabannin makarantun sakandare shida daga aiki a Sokoto

Jihar Ogun ta Nijeriya ta rufe kamfanonin ‘yan China biyar kan tsangwamar jami’an gwamnati

Ma’aikatan FIRS huɗu da na UCP 6 sun rasa rayukansu a gobarar wani babban ofis a Legas

Aƙalla ɗalibai 1,400 aka yi garkuwa da su tun bayan Boko Haram ta sace ‘yan matan Chibok — MDD
17 Sep, 2025
Saudiyya ta saki ‘yan Nijeriya uku da ta tsare bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi
Daraktan yada labarai da yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa sakin nasu ya biyo bayan wata yarjejeniya tsakanin hukumar ta NDLEA da gwamnatin Saudiyya.

17 Sep, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta kai ƙarar Sowore da Meta da X kotu kan cin fuskar Tinubu
Lauyoyin Sowore sun ƙara da cewa dole Meta da X su gane cewa a muddin suka yi biyayya ga buƙatar gwamnatin Nijeriya ta hana tofa albarcin baki, to sun saɓa wa doka kuma sun zama masu hannu a laifin danne gwagwarmayar samun ‘yanci.

17 Sep, 2025
Yayin da ake yarjejeniyar zaman lafiya a Katsina: ‘Yan ta’adda sun sace mutum 55 a Zamfara
Wasu masana na ganin idan ana so a magance matsalar tsaro a arewa maso yammacin Nijeriya, ya kamata gwamnatoci su yi sulhu da ‘yan bindiga a yankin, yayin da wasu ke ganin sulhu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba.

16 Sep, 2025
Hauhawar farashi a Nijeriya ta ragu karo na biyar a jere – NBS
Alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa hauhawar farashin ta ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 daga kashi 21.88 cikin 100 da ta kasance a watan Yuli.

16 Sep, 2025
Motocin Dangote na CNG sun fara lodin mai a matatarsa don yin dakonsa kyauta a faɗin Nijeriya
Wakilan kafafen yaɗa labarai da dama na Nijeriya da suka halarci ƙaddamarwar a ranar Litinin sun ce tuni rukunin farko na motocin suka hau layi don yin lodin man.

15 Sep, 2025
Mutum 19 ‘yan ɗaukar amarya sun rasu bayan motarsu ta faɗa cikin kogi a Zamfara
Motar ta faɗa cikin a kogin ne a lokacin da take yunƙurin tsallake wata gada da ta karye wadda ke tsakanin ƙauyen Gwalli da garin Gummi a Jihar Zamfara.

12 Sep, 2025
Gwamnatin Jihar Kano ta goyi bayan ƙudurin haramta auren jinsi
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 31.

12 Sep, 2025
Likitoci masu neman ƙwarewa sun tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya
Matakin ya biyo bayan cikar wa’adin sa’a 24 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya cewa ta biya bukatunta.

12 Sep, 2025
Babu gudu babu ja da baya kan dakon mai kyauta a Nijeriya— Matatar Dangote
Wata sanarwa da matatar ta fitar ranar Alhamis ta ce ruɓanya farashin gas din ba zai hana ta fara amfani da tankoki 10,000 domin dakon mai kyauta a fadin Nijeriya ba.

12 Sep, 2025
Kotun Nijeriya ta ɗaure shugaban ƙungiyar Ansaru shekara 15 kan ta’addanci
Mahmud Usman ya amsa laifin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba inda yake amfani da kuɗinsu wajen sayen makamai domin kai hare-haren ta’addanci da yin garkuwa da mutane.



