6 Sep, 2025

‘Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC, sun yi garkuwa da wani ɗan China

Majiyoyi sun ce maharan sun buɗe wuta kan jami’an ne inda suka kashe takwas daga cikinsu nan-take. Sun kama ɗaya daga cikin ‘yan China, yayin da huɗu suka tsallake rijiya da baya.

577048a23bc865d5516d297dd6a99efcf3026e6cb0b68ae2ccff425d93b56d1c

5 Sep, 2025

DSS ta gurfanar da shugabannin Ansaru da ‘ke da alaƙa da fasa gidan yarin Kuje’ da laifin ta’addanci

A cewar hukumar ta sirri, laifukan da ake tuhumar su da su sun hada da jagorantar kungiyar ta’addanci, ba da kudaden gudanar da ayyukanta, da daukar ma’aikata, da kuma shirya ayyukan tarzoma a fadin kasar.

fe3ace07012ad4c6a144299f629d0e39573ef92235eb3ec8519d8a152f7cba08

4 Sep, 2025

Shugaba Tinubu ya tafi Faransa da Ingila don fara hutun shekara-shekara na kwana 10

A watan Oktoban shekarar 2024 ma shugaban na Nijeriya ya tafi hutun shekara-shekara na mako biyu.

Tinubu

4 Sep, 2025

Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum 60 a Jihar Neja ta Nijeriya — Hukumomi

Fiye da mutum 100 ne a cikin kwale-kwalen lokacin da ya daki wani kututture da ke ƙarƙashin ruwa sannan ya kife a Jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.

404342dc10b0c3a901b557434248cfff8f75b09616e3d0f5af7ba873c0ec05a6

3 Sep, 2025

Gwamnatin Nijeriya da Majalisar Dokoki sun goyi bayan tsarin mai da rubuta jarabawar WAEC ta komfuta

Wannan babban sauyin, wanda aka tsara cewa zai fara aiki a shekarar 2026 ya jawo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.

3fa13d272ce2dee8b6ecf0e3ce51e44c018d2d69d92f6a1d1bd76a34ec5024c0

3 Sep, 2025

Tinubu ya amince a sayi ƙarin jirage mara matuƙa don yaƙi da ‘yan bindiga a Arewacin Nijeriya

Kwanan baya ne Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya halarci baje-kolin kayayyakin yaƙi da ƙere-ƙere na duniya a Istanbul inda Turkiyya ta amince ta sayar da ƙarin jirage mara matuƙa da horas da sojojin Nijeriya kan dabarun yaƙi na zamani.

30fa9fa18826fb62ed7958e59aebdb2c7cdf8bc90d5cdad1ddb99ed456973283

2 Sep, 2025

Ban yi kuskure ba wajen ɗaukar Shettima a matsayin mataimakina, in ji Tinubu

A shekarar 2023 ne aka zaɓi Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a matsayin shugaba da mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, sai da an yi ta raɗe-raɗin cewa Tinubu zai ajiye Shettima a zaɓen 2027.

62d2b3ef35e7a2d36a46a16565da0f4f1de283958f4b921bed8a1204ccfe38ef

1 Sep, 2025

Nijeriya ta ƙaddamar da sabuwar manhajar karatu a matakin farko da babbar sakandare da ilimin fasaha

“Sabon tsarin zai kawo daidaito a darussan da ake koyarwa wajen zurfafawa da kuma koyar da ilimi a aikace.

f551e643b1cbc7e8c3536df636f525287c1c643bded28c5fb2fd2799a9e610b8

1 Sep, 2025

Nuhu Ribadu ya mayar wa El-Rufai martani kan zargin cewa gwamnati na biyan ‘yan ta’adda kuɗaɗe

Mai magana da yawun Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Malam Zakari Mijinyawa ya ce kalaman na tsohon gwamnan ba gaskiya ba ne.

445f6ba64fa46f1c9e1ad9e1422bef9d1badfe94ab8eed1a69692beaabcb01d9

1 Sep, 2025

Sojojin Nijeriya sun kashe ’yan ta’adda 12 a Mafa da ke Borno

Sojojin sun samu nasara ne bayan sun samu bayanan sirri da kuma bayanai daga na’urorin leƙen asiri na Rundunar Sojin Sama, waɗanda suka samar da bayanai kai tsaye domin aiwatar da luguden wuta kan ‘yan ta’addan.

1a4f9b4c1c9c1a6c3bc5bc012fa875559124e619335e24c4c9e066d273eb5bdd
Ana lodawa...