Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi

Farashin ya ragu zuwa Naira 800,000 ($521) kan kowane ton a ranar Alhamis, wanda ya yi ƙasa da kashi 33 cikin ɗari daga farashin da aka sayar kwanaki kaɗan da suka gabata.
30 Aug, 2025
Yara ‘yan Najeriya 420,000 na fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki a bana – UNICEF

Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Elfadil Saeed Abdelatef ce ta yi wannan gargadin a lokacin ziyararta ofishin UNICEF na Maiduguri a ranar Alhamis.
29 Aug, 2025
Dakarun sojin Nijeriya ‘sun kashe ‘yan bindiga 50’ a Jihar Neja

‘Yan bindiga kusan 300 ne suka yi yunƙurin kutsawa ƙauyen Kumbashi da misalin karfe 3 na ranar Talata amma jami’an rundunar soji da na rundunar farin kaya ta DSS sun tunkare su, in ji shugaban Majalisar jihar ta Neja.
29 Aug, 2025
‘Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan 1.3 wajen sayen fetur a watan Yuni — NMDPRA

Hukumar kula da harkokin sarrafawa, tacewa da sufurin man fetur ta Nijeriya, NMDPRA ce ta tabbatar da hakan inda ta ce
28 Aug, 2025

‘Yan Nijeriya sun biya N2.57b a matsayin kuɗin fansa a cikin shekara ɗaya: Rahoto

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kafa kwamitin bincike kan hatsarin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Amurka ta ɗaure wani mai sarauta a yankin Yarabawa na Nijeriya kan zambar $4.2M na tallafin Covid-19

Shugaba Tinubu ya dakatar da fitar da ƙwallon kaɗanya daga Nijeriya

ECOWAS za ta kafa runduna mai dakaru 260,000 don yaƙar ta’addanci
26 Aug, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta gabatar da mutum 128 da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga a jihar Zamfara
Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu ne ya gabatar da mutanen da aka ceto ɗin ga manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.

26 Aug, 2025
Jirgin ƙasan Kaduna-Abuja na Nijeriya ya yi hatsari bayan sauka daga layinsa
Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya ba ta ce komai a kan lamarin ba, sannan ba a san musabbabin faruwar hatsarin ba.

26 Aug, 2025
Abin da ya sa PDP ta miƙa wa Kudancin Nijeriya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 – Gwamna Bala
Gwamna Bala Mohammed ya ce ‘yan Nijeriya ne suke kira ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya dawo mulki, ba Jam’iyyar PDP kawai ba.

25 Aug, 2025
NDLEA ta kama ƙasurgumin mai safarar ƙwaya da mutum 5 kan kama ‘yan Nijeriya 3 da aka yi a Saudi
A makon da ya wuce ne hukumomin Saudiyya suka kama mutum ukun a birnin Jeddah bayan gano miyagun ƙwayoyi a cikin kayansu.

25 Aug, 2025
NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama mai ƙarfi da tsawa na kwanaki uku a Nijeriya
“Za a iya samun ambaliya a jihohin Bauchi da Jigawa da Katsina da Kaduna da kuma Kano a wannan lokacin,” in ji sanarwar NiMet.

25 Aug, 2025
Dai Qisheng: Nijeriya ta tasa ƙeyar ƙasurgumin ɗan daba da ake nema ruwa-a-jallo a China
Mista Dai Qisheng ƙasurgumin shugaban ‘yan daba ne da ake nema ruwa-a-jallo a China.

24 Aug, 2025
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 76 da aka sace a Jihar Katsina
Sojojin Saman Nijeriya ne suka samu wannan nasara a yankin Karamar Hukumar Kankara yayin wani aiki na yunkurin kamo wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Babaro, wanda ake zargi da hannu a wani mummunan hari kan masallata a makon da ya gabata.

24 Aug, 2025
Sojojin Saman Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 35 a kusa da iyakar ƙasar da Kamaru
Hare-haren, waɗanda aka kaddamar da su da safiyar Asabar, 23 ga Agustan 2025, an aiwatar da su ne ƙarƙashin Operation Hadin Kai (OPHK), bayan wani yunƙurin kai hari da ‘yan ta’addan suka yi kan dakarun ƙasar a Kumshe da ke Jihar Borno.

23 Aug, 2025
Tinubu ya yi alƙawarin hanzarta ƙera makamai da harsasai a cikin Nijeriya saboda tsaro
Shugaba Tinubu wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kashim Shettima a Kwalejin Tsaro ta Nijeriya da ke Abuja, ya yi alkawarin hanzarta ƙera makamai da harsasai a cikin gida domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar da kuma rage dogaro da ƙasashen waje.

22 Aug, 2025
Ibrahim Bakura: Rundunar Sojin Nijar ta ce ta kashe wani jigo a Boko Haram
Taƙaitacciyar sanarwar da rundunar sojin ta Jamhuriyar Nijar ta fitar ta bayyana harin sama na sojin a matsayin wanda ba a saba kai irinsa ba.



