Hukumar INEC ta Nijeriya ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da makwanni biyu

Hukumar INEC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan la’akari da ra’ayoyin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin fararen-hula da sauran masu ruwa da tsaki.
4 Jul, 2026
Kotu ta samu mutum biyu da laifin ta’addanci a Nijeriya

Rundunar ‘yansandan ƙasar ta ce an fara sharia’r mai alaƙa da ta’adanci ne a jihar Katsina bayan an kama mutanen a wani babban samame kan safarar makamai a watan Satumbar 2025.
4 Jul, 2026
Nijeriya ta ƙaddamar da masana’antar sarrafa lithium mafi girma a Yammacin Afirka a jihar Nassarawa

Masana’antar, wacce Kamfanin Avatar New Energy Materials ya gina, ana sa ran za ta sarrafa ma’adinan lithium zuwa kayayyaki masu daraja don amfani da su a cikin batirin motocin lantarki da sauran fasahar makamashi mai tsabta.
3 Jul, 2026
Amurka ta janye akasarin sojojinta da ta aika Nijeriya

Kwamandan Rundunar Amurka ta Afrika (AFRICOM) ne ya sanar da batun janyewar a ranar Alhamis inda ya ce an janye dakarun ne tun bayan harin da aka kai a watan Mayu wanda ya kashe Abu-Bilal al-Minuki, mataimaki na biyu a jagorancin ƙungiyar Daesh.
3 Jul, 2026

Yunwa ta kai mummunan mataki da bai taɓa kai wa ba a shekaru 10 a Arewacin Nijeriya – WFP

Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 662, sun ceto 951 da aka sace cikin watanni uku

CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji

Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa ‘yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu

Gwamnatin Nijeriya ta karɓi ‘yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga Afirka ta Kudu
30 Jun, 2026
Jam’iyyar adawa ta NDC a Nijeriya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu game da rijistarta
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wata babbar kotun tarayya a birnin Lokoja ta jihar Kogi, ta jingine hukuncin da ta yanke daga farko da ya bai wa hukumar zaɓe (INEC) umarnin yi wa NDC rijista a matsayin jam’iyyar siyasa.

29 Jun, 2026
‘Yanta’addan Boko Haram sun kai hari makaranta sun kashe malami tare da sace dalibai a Jihar Borno
Sun yi ta buɗe wuta , inda suka kashe malami ɗaya da kuma ji wa wasu mutane ciwo kafin su yi garkuwa da wasu ɗalibai da ba a san adadinsu ba

29 Jun, 2026
Dakarun Nijeriya sun ce manyan kwamandojin DAESH sun miƙa wuya sakamakon ƙara matsin lambar soji
Rundunar ta ce ana tsare da waɗanda suka miƙa wuya a wani wuri mai tsaro, inda ake tantance su, yi musu tambayoyi da kuma gudanar da sauran matakan da suka dace bisa ƙa’idojin aikin soji.

29 Jun, 2026
An kama mutane 10 da ake zargi da kashe shugaban ƙungiyar Fulani ta MACBAN na jihar Benue a Nijeriya
An kama wadanda ake zargin ne a daren 27 ga Yuni a yayin wani aiki samame da tawagar sashen dabaru na rundunar ta gudanar a karamar hukumar Otukpo, in ji mai magana da yawun yansanda jihar Benue.

28 Jun, 2026
Sojoji sun kashe Lakurawa biyu da ƙwato makamai a Arewa Maso Yammacin Nijeriya
A cewar rundunar sojin, an ƙaddamar da aikin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa waɗanda ake zargin na shirin kai hari kan al’ummar Sabarumawa.

28 Jun, 2026
DSS ta saki mutumin da aka tsare saboda zargin alaƙa da Boko Haram bisa kusure, ta biya shi diyya
Jaridun Nijeriya sun rawaito cewa Shugaban DSS ne ya bayar da umarnin sakin manomin, Nura Idris, wanda kuma makiyayi ne daga Karamar Hukumar Soba ta jihar Kaduna, yayin da ake ci gaba da nazari kan batutuwan waɗanda aka tsare ba bisa ƙa’ida ba.

27 Jun, 2026
‘Yanbindiga a Nijeriya sun kashe manoma 17 a Jihar Zamfara
Yanbindiga kan babura da dama sun kai hari ƙauyen Tungar Baure a Jihar Zamfara inda suka buɗe wuta a ranar Jumma’a, in ji Yahaya Abubakar Yari, mai kula da harkokin siyasa na Karamar Hukumar Talata Mafara.

27 Jun, 2026
An gurfanar da ƙarin mutum 17 bayan tuhumar 33 bisa zargin kisan Malamar Islamiyya a Kaduna
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu a ranar 25 ga Yuni, 2026.

26 Jun, 2026
Sojojin Nijeriya sun ceto fararen-hula 53 tare da ƙwato motoci takwas a Borno
Dakarun sojin Nijeriya sun samu nasarar ceto fararen-hular bayan sun tarwatsa wani shinge da ‘yanta’adda suka kafa a Hanyar Buratai zuwa Kamuya a Jihar Borno.

26 Jun, 2026
Mutum aƙalla takwas sun mutu, an ceto 26 bayan bene mai hawa uku ya rushe a Legas
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta bayyana cewa jami’an ba da agajin gaggawa sun samo gawarwaki takwas kuma sun ceto mutum 26 daga ɓaraguzan ginin zuwa misalin ƙarfe 4:20 na yammacin ranar Alhamis.



