Nijeriya

NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama mai ƙarfi da tsawa na kwanaki uku a Nijeriya

“Za a iya samun ambaliya a jihohin Bauchi da Jigawa da Katsina da Kaduna da kuma  Kano a wannan lokacin,” in ji sanarwar NiMet.

Newstimehub

Newstimehub

25 Aug, 2025

4a2411f845562506d5bac8dfeb235002c3628035aca76893eb4e29677e22c278

Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a yi ruwan sama ai ƙarfi da tsawa daga ranar Litinin zuwa ranar Laraba a faɗin ƙasar.

Hukumar, a wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, ta bayyana cewa za a yi tsawa da ruwa a jihohin arewacin Nijeriya ciki har da jihohin Jigawa da Zamfara da Kano da Kaduna da Bauchi da Yobe da kuma Katsina, farawa daga safiyar Litinin, inda ake tsammanin ruwan da za a yi da rana zai kai jihohin Kebbi da Adamawa da kuma Taraba.

“Za a iya samun ambaliya a jihohin Bauchi da Jigawa da Katsina da Kaduna da kuma  Kano a wannan lokacin,” in ji sanarwar.

“Jihohin tsakiyar Nijeriya da suka haɗa da Neja da Binuwe da Birnin Tarayya Abuja da Filato da kuma Nasarawa za su fuskanci hadari da ruwan sama da safiya da babbar barazanar ambaliya a wasu yankunan Filato.

“A kudu kuwa yayyafi zuwa matsakaicin ruwa za a yi a jihohin Ondo da Imo da Abia da Enugu da Ebonyi da Anambra da Edo da Delta da Bayelsa da Ribas da Cross River da kuma Akwa Ibom,” in ji NiMet .

Hukumar ta ce ranar Talata za a rana da hadari a arewa, yayin da ake hasashin za a yi tsawa da ruwa a wasu yankunan jihohin Adamawa da Taraba da wasu jihohi maƙwabta.