Nijeriya

Rashin sa ido kan shigar da mai Nijeriya na barazana ga ayyukan yi da zuba jari: Dangote

Dangote ya bukaci a gudanar da bincike na hukuma a kan Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA.

Newstimehub

Newstimehub

15 Dec, 2025

2025 11 12t162925z 63217581 rc28ggap24xm rtrmadp 3 zimbabwe investment dangote

Hamshaƙin attajirin Nijeriya, Aliko Dangote, ya zargi masu kula da harkokin man fetur na ƙasar da ba da damar shigar da mai ƙasar cikin rahusa, yana mai cewa hakan na barazana ga matatun mai na gida, sannan ya yi kira da a gudanar da bincike.

Nijeriya ita ce babbar mai samar da mai a Afirka, amma tana dogaro sosai da shigar da man, kuma an kafa matatar Dangote ne don magance wannan matsalar.

Dangote ya ce idan aka bari ana shigar da mai ƙasar ba tare da saka ido ba, hakan zai zama barazana ga ayyukan yi, zuba jari, da tsaron makamashi.

Yayin da yake magana a matatarsa da ke Lagos wadda ke da ƙarfin sarrafa ganga 650,000 a rana, Dangote ya ce ana amfani da shigo da mai daga ƙasashen wajen don yin ƙafar ungulu ga masana’antun cikin gida.

Kira don gudanar da bincike

“Ba za a yi amfani da shigo da mai daga waje don daƙushe cikin gida ba,” in ji shi ga ‘yanjarida.

Dangote ya bukaci a gudanar da bincike na hukuma a kan Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA.

Sai dai NMDPRA ta zargi matatar Dangote da son samun mallakar kasuwa wajen sayar da dangogin mai, amma abin da matatar ke fitarwa ba zai iya gamsar da bukatun cikin gida ba.

A watan da ya gabata, hukumar ta bukaci shugaban ƙasa da ya daina shirin haramta shigo da dangogin mai da aka riga aka tace saboda fitar da kayayyakin cikin gida ba zai iya gamsar da bukatar ƙasa na lita miliyan 55 a kowace rana ba.

Dangote ya musanta wannan, yana cewa hukumar na karkatar da ainihin ƙarfin matatar ta hanyar ba da kididdigar abin da ake karba (offtake) maimakon bayanan hakikanin abin da take samarwa.

Rashin isasshen dangogin mai

Matatar, wacce aka tsara don kawo karshen dogaro da shigo da mai da kuma ceton biliyoyin kuɗaɗen musayar kasashen waje, ta ce ba ta sami damar samun duk danyen mai da take bukata ba saboda hukumar ba ta aiwatar da doka da ke tabbatar wa matatun cikin gida samun danyen mai kafin a fitar da shi ba.

Dangote ya ce matatar na shigo da ganga miliyan 100 na danyen mai a shekara — adadin da ake sa ran zai ninka bayan fadada matatar da kuma iyakacin samarwar cikin gida.

Duk da waɗannan matsalolin, Dangote ya yi alkawarin ci gaba da shirin fadada wurin da kuma kare jarinsa, wanda ya ce “mai girma ne da ba zai gaza ba”.

Har ila yau ya maimaita shirin jera kamfanin a kasuwar hannayen jari ta cikin gida da biyan riba a cikin dalar Amurka domin “kowannen ɗan Nijeriya ya iya mallakar wani ɓangare na tattalin arzikin”.

Nijeriya, ƙasar da ta fi samar da mai a Afirka, ta dade tana dogaro da shigo da mai saboda matatunta da suka daina aiki.