Mai Martaba Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, Sarkin Qatar, da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio sun gana a Doha, inda suka tattauna kan dangantakar dabarun kasashensu da harin Isra’ila a kan Doha, da kuma yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza, in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Majed al-Ansari ya bayyana cewa tattaunawar ta kuma tabo batun harin Isra’ila da aka kai makon da ya gabata a Doha.
“Dangantakarmu da Amurka tana da mahimmanci sosai, musamman a matakin tsaro,” in ji Al-Ansari a wata sanarwa da aka wallafa ta hanyar Al Jazeera.
Ya jaddada cewa Qatar ta kuduri aniyar kare ‘yancinta da daukar matakan da za su hana irin wannan hari maimaituwa.
Al-Ansari ya kara da cewa Doha tana godiya ga goyon bayan da kasashen Larabawa da na Musulmi suka nuna a matsayin hadin kai da Qatar bayan harin Isra’ila.
Ya kuma bayyana cewa Washington ta samu labarin kai harin mintuna 50 kafin ya faru, amma ya kara da cewa, “Ba ma dogara da rahotannin kafafen yada labarai; muna magana kai-tsaye da Amurka.”
“Sakonmu ga Netanyahu shi ne cewa ba za mu lamunci karya dokokin kasa da kasa ba,” in ji Al-Ansari.
Game da yiwuwar tattaunawa, mai magana da yawun ya ce tattaunawar “ba ta da ma’ana a yanzu, domin Netanyahu yana son kashe duk wanda ya shiga tattaunawa da shi kuma yana kai hari ga kasar da ke shiga tsakani.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana cewa Rubio ya sake jaddada “karfin dangantakar kasashen biyu” tsakanin Amurka da Qatar kuma ya gode wa Doha “saboda kokarinta na kawo karshen yakin Gaza da dawo da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su.”
Babban jami’in diflomasiyyar ya kuma jaddada “karfin goyon bayan Amurka ga tsaro da ‘yancin Qatar da kuma tattauna alkawarinmu na bai-daya don samun yankin da ya fi aminci da kwanciyar hankali,” in ji sanarwar.
Ziyarar Rubio ta gajeren lokaci zuwa Qatar ta biyo bayan ziyararsa zuwa Isra’ila, inda ya yi tattaunawa da Netanyahu.
Kafin isarsa Qatar daga Isra’ila, Rubio ya bayyana cewa Washington da Doha suna gab da kammala wata yarjejeniya mai karfi kan hadin gwiwar tsaro.
“Muna da kyakkyawar dangantaka da Qatar,” in ji Rubio ga manema labarai kafin ya bar Tel Aviv zuwa Doha.
“A gaskiya, muna da wata yarjejeniya mai karfi kan hadin gwiwar tsaro, wadda muka dade muna aiki a kanta, kuma muna gab da kammalawa.”
Da yake magana kan rawar da Qatar ke takawa wajen shiga tsakani don tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza, Rubio ya ce, “Za mu bukaci Qatar ta ci gaba da abin da take yi.”














