An ji sautin gargadi a sassa daban-daban na Isra’ila, musamman a Tel Aviv, bayan Iran ta harba makamai masu linzami a matsayin martani ga hare-haren hadin gwiwa da Isra’ila da Amurka suka kai mata. Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo makaman daga Iran zuwa cikin yankin Isra’ila.
A cewar rundunar, an tura tsarin kariyar sararin samaniya domin kokarin tare makaman kafin su kai ga wuraren da ake zaune. Bayan harin, sautunan gargadi sun fara tashi a arewacin Isra’ila kafin daga bisani su bazu zuwa tsakiyar ƙasar, ciki har da Tel Aviv da kuma yankin Jerusalem.
Shaidu sun ce an ji karar fashewa a sararin samaniyar Tel Aviv yayin da tsarin kariyar Isra’ila ke kokarin lalata makaman da Iran ta harba.














