Fiye da shekaru 70, ƙasashe masu tasowa sun dogara da IMF da Bankin Duniya wajen samun lamuni da aiwatar da tsare-tsaren tattalin arziki. Sai dai a zamanin yau, ana ganin wasu ƙasashe musamman na Afirka na ƙoƙarin samun cikakken ‘yanci a harkokin tattalin arzikinsu ba tare da dogaro sosai da waɗannan cibiyoyin duniya ba. Wasu daga cikinsu, irin su Ethiopia da Kenya, sun juya zuwa China domin samun kuɗaɗen gina muhimman ayyukan ci gaba. Bugu da ƙari, kafa bankin ci gaban BRICS ya ba su wata sabuwar hanya da zaɓuɓɓuka masu yawa wajen neman tallafin kuɗi.
Sai dai, duk da waɗannan hanyoyin, har yanzu IMF ce cibiyar da ƙasashe ke dogaro da ita lokacin da suke cikin tsananin matsin tattalin arziki kamar yadda Ghana, Zambia, Sri Lanka da Pakistan suka fuskanta. IMF na bayar da bashi da shawarwari kan farashin musayar kudi da tsare-tsaren rage matsalolin tattalin arziki, yayin da Bankin Duniya ke mai da hankali kan manyan ayyuka irin su hanyoyi, asibitoci, ilimi da noma. Masana sun nuna cewa ƙasashe za su iya rayuwa ba tare da dogaro da IMF ba, amma hakan yakan yi wahala yayin da tattalin arziki ya shiga halin rikici.
Wasu ƙasashe suna ganin zaɓi mafi kyau shi ne neman sabbin alaƙa da ƙawancen tattalin arziki domin ci gaba, sai dai a zahiri babu ƙasa da za ta iya cigaba ita kaɗai ba tare da tallafi da haɗin kai ba. Masana irinsu Dr. Seydou Bocoum na ganin lokaci ya yi da ƙasashe masu tasowa za su daina dogaro da tsohon tsarin manufofin IMF (Washington Consensus) wanda ya nuna ba ya aiki yadda ya kamata a waɗannan ƙasashe.














