Shugaban gwamnatin Sudan al-Burhan ya naɗa Al-Haj a matsayin Firaminista

Kazalika Al-Burhan, wanda shi ne shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, ya naɗa fitaccen jami’in diflomasiyya Omer Mohamed Ahmed Siddiq a matsayin ministan harkokin wajen Sudan.

Newstimehub

Newstimehub

1 May, 2025

2025 04 30t150151z 1 lynxmpel3t0u3 rtroptp 3 sudan politics burhan 1

Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya naɗa Dafallah Al-Haj Ali a matsayin firaminista na riƙon ƙwarya kuma ministan majalisar gudanarwa ta ƙasar.

Al-Burhan ya bayyana haka ne a sanarwar da gwamnatinsa ta fitar ranar Laraba da maraice.

A halin yanzu Al-Haj shi ne jakadan Sudan a ƙasar Saudiyya kuma tun a shekarar 1980 yake aiki a Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar.

Ya riƙe muƙamin jakadan Sudan a Pakistan, Fadar Vatican da Faransa, sannan shi ne wakilin dindindin na ƙasarsa a Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai wato Organization of Islamic Cooperation (OIC) da Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ba a naɗa kowa a matsayin firaminsta ba tun bayan da tsohon firaminista Abdalla Hamdok ya sauka daga kan muƙamin a watan Janairu na shekarar 2022 bayan juyin mulkin da Al-Burhan ya jagoranta a watan Oktoba na 2021.

Kazalika Al-Burhan ya naɗa fitaccen jami’in diflomasiyya Omer Mohamed Ahmed Siddiq a matsayin ministan harkokin wajen Sudan da Dr. al-Tahami al-Zein Hajar Mohamed a matsayin Ministan Ma’aikatar Ilimi.