Gwamnatin Spain ta mayar da martani ga barazanar shugaban Amurka Donald Trump na cewa zai iya “dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci” da Spain. Madrid ta bayyana cewa duk wani sauyi da Amurka ke son yi a dangantakar kasuwanci dole ne ya kasance cikin girmama dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyoyin da ake da su tsakanin Amurka da Tarayyar Turai.
A wata sanarwa da kafar watsa labarai ta RTVE ta ruwaito, gwamnatin Spain ta jaddada cewa idan Washington na son sake nazarin dangantakar kasuwanci, to ya kamata hakan ya mutunta ‘yancin kamfanoni masu zaman kansu da kuma dokokin kasa da kasa.
Wannan martani ya biyo bayan sukar da Trump ya yi wa Spain, inda ya kira ta “aboki mara kyau” tare da zargin cewa Madrid ba ta bayar da cikakken hadin kai kan batun sansanonin sojin Amurka ba.
Sai dai gwamnatin Spain ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa Spain muhimmiyar mamba ce a kungiyar tsaron NATO kuma tana cika dukkan alkawurranta, tare da taka muhimmiyar rawa wajen kare yankin Turai.
Haka kuma ta jaddada cewa Spain babbar kasa ce mai fitar da kayayyaki zuwa kasashen duniya fiye da 195, ciki har da Amurka, inda suke da dadadden hadin gwiwar kasuwanci mai anfani ga bangarorin biyu.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa tana da hanyoyin da za ta rage duk wani tasiri idan aka samu matsalar kasuwanci, ciki har da tallafawa bangarorin tattalin arziki da ka iya fuskantar matsala da kuma fadada hanyoyin samar da kayayyaki. Madrid ta kuma sake jaddada cewa tana goyon bayan ciniki cikin ‘yanci da hadin kan tattalin arziki tsakanin kasashe bisa girmama juna da dokokin kasa da kasa.














