Shugaban Amurka Donald Trump ranar Jumma’a ya ce yana duba yiwuwar “kammala” hare-haren soji da ake kai wa Iran sannan ya ƙara da cewa sauran ƙasashe ne suka kamata su “bayar da kariya tare da sanya ido” kan Mashigin Hormuz saboda muhimmancinsa.
“Mun kusa cim ma muradunmu don haka muna duba yiwuwar kammala ayyukan da gwarazan sojojinmu suke yi a Gabas ta Tsakiya game da Gwamnatin Ta’addanci ta Iran,” a cewar Trump a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social.
“Ƙasashen da ke amfani da Mashigin Hormuz su ne suka kamata su ba shi kariya tare da sanya idanu a kansa — Amurka ba za ta yi bat!” in ji shi.
Lamura sun dagule a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare a Iran ranar 28 ga Fabrairu. Rahotanni sun ce hare-haren sun kashe aƙalla mutum 1,300, cikinsu har da ƙananan yara mata ‘yan makarantar firamare fiye da 150.
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da kuma kayayyakin Amurka da ke ƙasashen Larabawa, abin da ya ƙara yamutsa yaƙin.














